Shugaban kamfanin BUA, Abdul Samad Rabiu, ya yi hasashen cewa Naira za ta ragargaza Dala zuwa tsakanin N1,300 a dala 1 - N1,400 a dala 1 kaf...
Shugaban kamfanin BUA, Abdul Samad Rabiu, ya yi hasashen cewa Naira za ta ragargaza Dala zuwa tsakanin N1,300 a dala 1 - N1,400 a dala 1 kafin ƙarshen 2025.
Abdul Samad Rabiu ya bayyana hakan ne jim kaɗan bayan ganawarsa da Shugaba Bola Tinubu a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja a ranar Laraba.
Alhaji Abdul Samad Rabiu, BUA, ya ce darajar Naira za ta kara ƙarfi zuwa ƙarshen 2025.
Shugaban BUA ya ce, sauye-sauyen manufofin tattalin arziƙin Tinubu sun riga sun fara ba da sakamako mai kyau ga 'yan kasuwa da kuma darajar Naira.
Alhaji Abdul Samad ya ce, “Ina sa ran darajar musayar kuxi za ta ƙara ƙarfi. Ina tsammanin Naira za ta koma N1,300 zuwa N1,400 kafin ƙarshen shekara. Kuma wannan wani abu ne da ya kamata mu yi murna da shi."
Da yake bayani game da tasirin gyare-gyaren tattalin arziki na kwanan nan, shugaban na BUA ya lura cewa kamfanoni sun daina dogara kacokan ga Babban Bankin Nijeriya (CBN).
Ya ce, "Yanzu kamfanonin sun daina shiga CBN karbar kuɗin waje (FX), domin yawancinsu suna amfani da katin kuxi na yanar gizo da kuma tsarin banki na ƙasa da ƙasa.
“Don haka, dole ne mu yaba wa shugaban ƙasa da gwamnati, sauye-sauyensu suna samar da babban tubali na tsayuwar tattalin arziki, da kuma kyakkyawar makoma ga kamfanoni da 'yan Nijeriya baki ɗaya.
Game da hauhawar farashin kayayyaki da tsadar abinci, Abdul Samad Rabiu ya ce farashin kayayyaki ya faɗi a yanzu idan aka kwatanta da na shekarar da ta gabata.
Ya qarfafa jama’a da su kara haquri yayin da gwamnatin Tinubu ke ci gaba da aiwatar da gyare-gyare da za su qara saukar da farashin abinci.
"Idan ka duba farashin kayan abinci a bara da abin da muke da shi a yau, za ka ga cewa an samu ragi mai yawa a farashin dukkan kayayyaki.
"Don haka, ina ganin muna buqatar mu ɗan ƙara haƙuri. A fili, abubuwa suna inganta, kuma dole ne mu ci gaba da goyon bayan gwamnati"
Jim kaxan bayan rantsar da shi a shekarar 2023, Shugaba Tinubu ya haɗa tare da buɗe kasuwar musayar kuɗin waje don sakar wa Naira mara, inda ya haɗa manyan hanyoyin musayar kudi zuwa tsari ɗaya.
Tun da farko a watan Yulin wannan shekara, Abdul Samad Rabiu ya ce sababbin manufofin CBN sun kawar da buƙatar kamfanoni su riƙa yin dogon layi don neman kuxin waje (FX).
Ya soki tsarin canjin kuxi na baya, inda darajar musayar na hukuma ya yi ƙasa da na kasuwar bayan fage, yana mai cewa hakan ya haifar da gurvacewa da kuma iyakance damar samun kuɗin ga kamfanoni da yawa.
"Na yi magana makonnin da suka gabata cewa sau biyu kawai na hadu da gwamnan CBN na yanzu tun bayan naɗin sa, saboda babu buƙatar hakan.
"Amma kafin yanzu, nakan ziyarci CBN duk bayan sati biyu don neman kuɗin waje. Hakan kawai zan yi domin in tsira a wancan lokaci," inji BUA.
No comments