Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

UNGA80: Nijeriya Ta Nemi A Yafe Wa Ƙasashe Masu Tasowa Bashin Da Ake Bin Su

Shugaban Bola Ahmed Tinubu, ya yi kira ga ƙasashen duniya da su yafe bashi ga ƙasashe masu tasowa, yana mai cewa hakan hanya ce madaidaiciya...


Shugaban Bola Ahmed Tinubu, ya yi kira ga ƙasashen duniya da su yafe bashi ga ƙasashe masu tasowa, yana mai cewa hakan hanya ce madaidaiciya ta wanzar da zaman lafiya da ci gaba.

Tinubu, wanda Mataimakin Shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya wakilta, ya yi wannan kira ne a lokacin da yake gabatar da jawabin ƙasa a babban taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 80 a birnin New York.

“Muna buƙatar wani sabon tsarin doka mai ɗaurewa, makamancin kotun duniya ta kuɗi, da zai ba ƙasashe masu tasowa damar kubuta daga ɗaurewar tattalin arziki na dogaro da fitar da albarkatun kasa ba tare da sarrafawa ba,” in ji Tinubu.

Ya bayyana Lagos Action Plan da aka tsara shekaru da dama da suka gabata, wadda ta bayyana hanyar kaucewa bashi da dogaro da shi, tare da baiwa ƙasashe damar ƙirƙira daga cikin gida a fannoni kamar noma, ma’adinai da kuma sarrafa man fetur.

Shugaban ya yaba da ƙirƙirar African Continental Free Trade Area (AfCFTA), yana mai cewa hakan babban abin alfahari ne da zai ƙara haɗa kan ƙasashen nahiyar.

Ya kuma ce Najeriya ta tsaya tsayin daka wajen cimma Manufofin Cigaba masu Dorewa (SDGs), wanda a cewarsa, za a iya cimma hakan ne ta hanyar mai da hankali kan manyan manufofi na haɓakar tattalin arziki da bunƙasa arziki.

Dangane da harkokin Afirka, Tinubu ya ce Najeriya tana maraba da yunƙurin zaman lafiya a Jamhuriyar Demokraɗiyyar Congo, tare da jaddada cewa zuba jari na ƙasa da ƙasa zai iya kawo ƙarshen rikice-rikicen da suka shafi ma’adinai.

Ya ce saka hannun jari a bincike, haɓakawa da kuma sarrafa waɗannan ma’adinai a nahiyar Afirka zai taimaka wajen sauya tsarin samar da kayayyaki ga kasuwar duniya, tare da rage rikice-rikice tsakanin manyan ƙasashe.

Shugaban ya ƙara da cewa Najeriya da sauran ƙasashen Afirka sun yi nasarori a cikin shekarun baya-bayan nan wajen gyara harkokinsu na cikin gida.

“Idan aka samu sauye-sauye da za su ƙarfafa tsarin kuɗaɗen duniya, za mu iya kai wannan ci gaba mataki na gaba, inda kasuwanci, zuba jari da riba za su buɗe sabbin damammaki ga nahiyarmu.”


 

No comments