Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Ziyarar Shugaban Yanki Na Hukumar Kwastan Ga Cibiyar KACCIMA Ta Kano

Daga Ibrahim Muhammad, Kano Kwanturolan Hukumar hana fasa ƙwabri ta ƙasa mai kula da shiyyar Kano da Jigawa, Abubakar Dalhatu, ya ziyarci ci...


Daga Ibrahim Muhammad, Kano

Kwanturolan Hukumar hana fasa ƙwabri ta ƙasa mai kula da shiyyar Kano da Jigawa, Abubakar Dalhatu, ya ziyarci cibiyar ciniki da masana’antu da ma’adinai da aikin gona na Jihar Kano (KACCIMA).

Da yake zantawa da manema labarai, Kwanturolan ya bayyana cewa cibiyar na da matuƙar muhimmanci da amfani a harkokin 
kasuwancin jihar Kano.

Haka kuma Abubakar Dalhatu ya bayar da 
shawarwari masu muhimmanci waɗanda  za su taimaka wa kasuwanci da ‘yan kasuwar jihar Kano, kuma za su riƙa gabatar da ƙasidu da kuma sauraren koke-koken ‘yan kasuwar.

Daga nan ya yi nuni da cewa jami’an Hukumar tasa ta hana fasa ƙwauri, ba wai wasu mutane ne na daban ba, kamar sauran mutane suke, akwai masu gaskiya a cikin su da marasa gaskiya, kar yadda ya ke a su ma ‘yan kasuwar, akwai masu gaskiya da marasa gaskiya.

Alhaji Abubakar Dalhatu ya kuma bayyana cewa suna son su kawar da waɗansu kura-kurai da ke addabar ‘yan kasuwa, ta yadda kasuwanci zai ƙara bunƙasa da ci gaba a jihar Kano da yardar Allah.

Shi ma a nasa jawabin, shugaban cibiyar KACCIMA, Ambasada Usman Hassan Darma, ya nuna mutuƙar farin cikin sa da wannan ziyarar da Shugaban ya kawo masu, musammam akan  yadda za su ƙulla harkokin kasuwanci, da yadda  'yan kasuwa za su kiyaye ƙa'idodi na doka wajen shigowa da titar da kaya.
 

No comments