Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Sojoji Sun Umarci A Gudanar Da Cikakken Bincike Kan Fashewar Wani Abu A Masana’antar Sojoji Ta Kaduna

Rundunar sojoji ta ƙaddamar da aikin gudanar da bincike akan tashin bom da ya faru a masana’antar makaman sojoji (DICON) da ke Kaduna, wanda...



Rundunar sojoji ta ƙaddamar da aikin gudanar da bincike akan tashin bom da ya faru a masana’antar makaman sojoji (DICON) da ke Kaduna, wanda ya yi sanadin mutuwar mutum ɗaya da raunata wasu da dama.

Lamarin ya auku ne a safiyar jiya Asabar inda ya sa al’umma a yankunan kusa da wajen cikin tsoro da zaman ɗar-ɗar.

Shaidu sun bayyana al’amarin a matsayin abin tsoro da firgitarwa saboda da yadda aka ji ƙara sassa da dama na birnin Kaduna.

A wata takarda da Daraktan yaɗa labaran Hedikwatar Tsaro (DHQ), Birgediya Janar Tukur Gusau ya fitar, ya ce lamarin ya faru ne yayin da ake tsaka sa kwalema domin fitar da sinadaran ababen fashewa da wasu kayayyaki da suka lalace bayan jimawa ana ajiyar su.

Rundunar sojin ta tabbatar da faruwar lamarin inda ta ce ana bai wa waɗanda su jikkata magani a Asibitin sojoji na 44 Army Reference Hospital, Kaduna.

DHQn ta kuma tabbatar wa al’ummar Jihar Kaduna da ma Nijeriya baki ɗaya cewa tana kula tare da sanya ido a lamarin, saboda haka su kwantar da hankali yayin da matakan kariya masu tsauri ke cigaba da aiki a DICON.

Akan haka ne rundunar sojojin ta bada umarnin a gaggauta gudanar da bincike mai zurfi a kai domin kauce wa sake faruwar irin haka a nan gaba.

No comments