Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Shettima Zai Jagoranci Tawagar Nijeriya Zuwa Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

 Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, zai jagoranci tawagar Nijeriya zuwa taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 80 da za a gudanar a b...


 Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, zai jagoranci tawagar Nijeriya zuwa taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 80 da za a gudanar a birnin New York, da ke Amurka, daga ranar Litinin 22 ga Satumba zuwa Lahadi 28 ga watan. 

Wannan na zuwa ne bisa umarnin Shugaba Bola Tinubu, kamar yadda mai taimaka masa na musamman kan yaɗa labarai, Stanley Nkwocha, ya bayyana a wata sanarwa a Abuja.

A cewar sanarwar, Shettima zai halarci taron murnar cika shekara 80 da kafuwar Majalisar Ɗinkin Duniya a ranar Litinin 22 ga Satumba, sannan daga ranar Talata 23 zuwa Lahadi 28 zai shiga tattaunawar manyan shugabanni a zauren babban taro. 

Haka kuma, a ranar Laraba 24 ga Satumba ne zai gabatar da jawabin ƙasa na Najeriya tsakanin ƙarfe 3 zuwa 9 na dare agogon New York.

Bugu da ƙari, Shettima zai shiga taro na musamman kan sauyin yanayi da Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya zai jagoranta a ranar 24 ga Satumba, inda Najeriya za ta sanar da sabbin manufofin ta bisa yarjejeniyar Paris. 

Haka kuma zai halarci taron manyan shugabanni kan samar da gidaje masu araha da shugaban Kenya zai shirya.

Bayan kammala taron Majalisar, Shettima zai zarce Frankfurt a ƙasar Jamus domin ganawa da jami’an Deutche Bank kafin ya dawo gida Najeriya.

No comments