An shiga tashin hankali a Masana'antar Ƙera Makaman Yaƙi ta Nijeriya (DICON) da ke cikin garin Kaduna lokacin da wani abun fashewa ya ta...
An shiga tashin hankali a Masana'antar Ƙera Makaman Yaƙi ta Nijeriya (DICON) da ke cikin garin Kaduna lokacin da wani abun fashewa ya tarwatse.
Rahotanni sun nuna cewa abin fashewar, wanda aka fara zaton bom ne da farko ya hallaka ma'aikata biyu a masana'antar yau Asabar, 20 ga watan Satumba, 2027.
Wannan lamari dai ya tada hankulan mutanen a kewayen masana'antar, wacce ke Unguwar Kurmin Gwari a cikin birnin Kaduna.
Kamfanin dillancin labarai na Nijeriya NAN ya bayar da rahoton cewa, lamarin wanda ya faru ne a lokacin da ake gudanar da aiki a ƙarshen mako a masana'antar, ya yi sanadin mutuwar ma'aikata biyu ciki, har da wani jami'in soji da ke aiki tare da jikkata wasu huɗu.
"Na ji wani babban ƙara har sai da ya girgiza gine-ginen da ke kewayen DICON. Mutane na ta gudu daga wurin, amma muna tunanin fashewar bam ne, amma daga baya mun gano cewa daga masana'anta ne," in ji wani mazaunin da ya nemi a sakaya sunansa.
Shaidun gani da ido sun ce fashewar na da nasaba da samar da hoda mai matukar muhimmanci wajen ƙera hodar harsashi ga sojojin Nijeriya.
No comments