Rundunar ’Yan Sandan Nijeriya ta ce aƙalla mutane 1,666 mazauna jihar Legas sun rasa ransu ta hanyoyin da ba su dace ba, ciki har da kashe k...
Rundunar ’Yan Sandan Nijeriya ta ce aƙalla mutane 1,666 mazauna jihar Legas sun rasa ransu ta hanyoyin da ba su dace ba, ciki har da kashe kansu, tsakanin farkon 2020 zuwa karshen 2024.
Wannan bayani ya fito ne daga bakin Likitan binciken gawarwaki na rundunar, ACP Samuel Keshinro, yayin gabatar da rahoton bincike kan kisan mata a wani taron da aka gudanar a jihar, ranar Alhamis.
A cewar Keshinro, rahoton ya mayar da hankali ne kan abubuwan da suka shafi kisan kai, kashe kai, hatsarurruka da sauran hanyoyin mutuwa da ba su da alaƙa da cuta, domin wayar da kan jama’a da ƙarfafa fafutuka kan matsalar kisan mata.
Bayanan da aka raba a wajen taron sun nuna cewa daga cikin mutuwar 1,666, 350 mata ne, yayin da 1,306 kuma maza ne, sai mutum 10 da ba a iya tantance jinsinsu ba.
Keshinro ya ce an tattara bayanan ne domin samar da madogara mai ƙarfi wajen yanke shawara da kuma wayar da kan jama’a kan hatsarin kisan mata.
Ya ce bayanan sun nuna cewa mafi yawan kisan mata ana aikata su ne daga abokan rayuwarsu na kusa.
“Mun fito da abubuwan da muka gano ta amfani da bayanan da ke hannun ’yan sanda a ofishin CID na jihar. Mun gano cewa daga cikin mutuwar mata 350, kusan guda 70 kisan abokan zamansu ne.
“Wannan yana nuna irin raunin da mata ke ciki, musamman a inda ake tsammanin za su samu ƙauna da kariya. Kuma ya zo a daidai lokacin da Majalisar Dinkin Duniya ta ware ranar 25 ga watan Nuwamba a matsayin ranar yaki da cin zarafin mata.”
Ya kuma ba da shawarar a rungumi amfani da tsarin adana bayanai ta kwamfuta da kuma inganta hanyoyin tattara bayanai a binciken laifuka.
A nasa jawabin, Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Legas, Olorundare Jimoh, ya bayyana cewa bisa ga bayanan da aka tattara cikin shekara guda, adadin kisan mata a jihar bai kai yadda ake tsammani ba idan aka kwatanta da yawan jama’ar jihar.
No comments