Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

UNGA: Nijeriya Ta Goyi Bayan Falasɗinu Su Gabatar Da Jawabi Ta Bidiyo Bayan Hana Su Visa Da Amurka Ta Yi

Nijeriya na ciki ƙasashe 144 da suka kaɗa ƙuri’a a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) domin bai wa Shugaban Falasɗinu, Mahmoud Abbas, dama...


Nijeriya na ciki ƙasashe 144 da suka kaɗa ƙuri’a a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) domin bai wa Shugaban Falasɗinu, Mahmoud Abbas, damar yin jawabi ta bidiyo a babban taron Majalisar bayan Amurka ta ƙi ba da visa ga tawagar sa.

An kaɗa ƙuri’ar ne a New York, inda aka samu ƙuri’u 145 na amincewa, ƙasashe biyar suka ƙi (ciki har da Amurka da Isra’ila), yayin da ƙasashe shida suka ƙaurace wa kaɗa ƙuri’ar. 

Wannan matakin zai bai wa Abbas damar aiko da jawabin sa da aka riga aka ɗauka ta bidiyo, wanda wani wakilin Falasɗinu a New York zai gabatar a dakin taron. Haka kuma an amince a yi amfani da wannan tsari na jawabin bidiyo ko ta haɗin kai tsaye (live) a wasu muhimman taruka na MDD, amma a abin da ya shafi zaman majasar karo na 80 kawai.

 

No comments