Jami’ar European-American ta yi ƙarin haske kan bikin karrama mawaƙi Dauda Kahutu Rarara a Abuja. Jami'ar ta fitar da sanarwa tana nesan...
Jami’ar European-American ta yi ƙarin haske kan bikin karrama mawaƙi Dauda Kahutu Rarara a Abuja.
Jami'ar ta fitar da sanarwa tana nesanta kanta daga digirin girmamawa da aka ba shahararren mawaƙi Dauda Kahutu Rarara.
Jami'ar ta wallafa a shafinta na yanar gizo cewa kwata-kwata ba ta da hannu a karramawar da aka yi wa Rarara.
Makarantar ta nesanta kanta daga mawaki Rarara da wadanda suka gabatar kansu a matsayin jami’an makarantar.
Sanarwar ta ce, "Jami’ar ba ta amince da kowanne taron karramawa a Abuja ba, an shirya shi ba tare da saninta ko yardarta ba."
Jami’ar ta ce, waɗanda suka shirya taron sun yaudari mutane, suna kiran kansu wakilan jami’ar, amma ba su da hurumin wakilta ko karbar kuɗi.
Ta ƙara da cewa,"Ba mu ba Dauda Kahutu Rarara, Ahmed Saleh Jnr., Mustapha Abdullahi Bujawa, ko Tarela Boroh digirin girmamawa ba."
Makarantar ta ce, ana samun sunayen masu digiri ne a rajistar malamai a shafinta, waɗanda aka ambata ba su cikin jerin sahihai.
An kuma bayyana cewa Musari Audu Isyaku wanda aka ce wakilin Arewa ne, babu hurumin wakiltar makarantar, don haka maganar bogi ce.
Haka kuma aka ce Idris Aliyu wanda aka bayyana a jarida a matsayin ɗan majalisar makarantar, ba ya daga cikin shugabannin makarantar.
Jami’ar ta ce, Aliyu Idris wanda aka bai wa matsayi a 2024, an cire shi nan take saboda rawar da ya taka a lamarin bogin.
Makarantar ta kuma tuna sanarwar da ta fitar a Afrilu cewa tsohuwar shugabar jami'ar, Josephine Egbuta, ta rasa hurumin wakiltar jami’ar.
Jami’ar ta ƙara bayyana cewa, yanzu shugaban makarantar shi ne Farfesa Luca Scotto di Tella de’ Douglas di Castel di Ripa.
Ta bayyana matsayinta na doka a Faransa da kuma samun 'Royal Charter' daga Bunyoro-Kitara, ta nesanta kanta daga iƙirarin Panama da Dominica.
Sanarwar ta kammala da cewa jami’ar za ta tuntubi hukumomin Nijeriya domin su dakile masu fitar da takardun bogi tare da gurfanar da su.
No comments