Shugaban Iran Masoud Pezeshkian, ya ce matakin da kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya dauka jiya Juma'a na sake kakaba wa kasar...
Shugaban Iran Masoud Pezeshkian, ya ce matakin da kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya dauka jiya Juma'a na sake kakaba wa kasarsa dukkanin takunkumin da ya danganci shirinta na nukiliya, ba zai hana kasar bunkasa shirin ba.
Ya kara da cewa, kwamitin tsaron ya rufe dukkanin kafofin diflomasiyya - kuma hakan ba zai zama wani gargadi ba.
Dangane da harin da Isra'ila da Amurka suka kai kan cibiyoyin nukiliya na Iran din a watan Yuni, shugaban ya ce - a duk lokacin da suka kai wa cibiyoyin hari, Iran za ta sake gina wadanda suka fi na baya - wadanda aka kai wa harin.
Rasha ta yi suka kan matakin kwamitin tsaron na sanya wa kawarta takunkumin - tana mai gargadin cewa ba abin da hakan zai haifar illa zaman tankiya.
No comments