Birtaniya ta sanar da amincewa da Falasɗinu a matsayin ƙasa mai 'yanci. "A yau, domin dawo da shirin samar da zaman lafiya tsakanin...
Birtaniya ta sanar da amincewa da Falasɗinu a matsayin ƙasa mai 'yanci.
"A yau, domin dawo da shirin samar da zaman lafiya tsakanin Falasɗinawa da Isra'ila, da kuma samar da ƙasa biyu, Birtaniya ta amince da ƙasar Falasɗinu a hukumance," a cewar Firaministan Birtaniya Keir Stermer cikin wani jawabi.
Firaministan Canada Mark Carney ya ce daga yau (Lahadi) "Canada ta amince da ƙasar Falasɗinu" a hukumance.
Cikin wata sanarwa da ya wallafa a dandalin X, Mista Carney ya ce:
"Canada ta amince da ƙasar Falasɗinu kuma muna miƙo tayinmu na taimakawa wajen samar da zaman lafiya tsakanin Falasɗinawa da Isra'ila."
Ita ma ƙasar Australia ta sanar da amincewa da ƙasar Falasɗinawa, inda ta bi sawun Birtaniya da Canada.
Kafin yanzu, ƙasashen Canada da Ausrtralia sun bayyaa a baya cewa sai a taron Majalisar Ɗinkin Duniya za su bayyana amincewa da ƙasar ta Falasɗinu, wanda za a fara a gobe Litinin.
No comments