Gwamnatin Tarayya ta fara bincike a ɗakin gwaje-gwaje domin gano musabbabin barkewar wata sabuwar cuta da ke cin naman mutum a Adamawa. An r...
Gwamnatin Tarayya ta fara bincike a ɗakin gwaje-gwaje domin gano musabbabin barkewar wata sabuwar cuta da ke cin naman mutum a Adamawa.
An ruwaito cewa, cutar, wadda ta bulla a garin Malabu, da ke karamar hukumar Fufore, ta kashe akalla mutane bakwai zuwa yanzu.
Dr Adesigbin Olufemi, mukaddashin kwamishinan shirye-shiryen kula da cututtuka irin su tarin fuka, Buruli Ulcer da kuturta, ya bayyana hakan a hira da NAN a Abuja.
Ya ce, daga ranar 10 ga Satumba, an tabbatar da cutar a jikin mutane 67, inda aka yi wa takwas daga cikinsu tiyata a Asibitin Koyarwa na Modibbo Adama, da ke Yola.
Rahotanni sun nuna cutar kan fara da kuraje masu ruwa, daga bisani ta fashe ta fara cin naman jiki, wani lokaci har ta lalata ƙashi.
Dr. Olufemi ya bayyana cewa har yanzu ba a tabbatar da musabbabin cutar ba, amma ana zargin Buruli Ulcer ce, wacce cutar Mycobacterium ulcerans ke haifarwa.
Ya ce, wannan kwayar cuta na rayuwa ne a wuraren da ruwa ke taruwa, da kogunan da ba sa gudana, kuma har yanzu ba a gano yadda ake yada cutar ba.
Muƙaddasshin ya yaba da yadda gwamnatin Adamawa, tarayya, kungiyoyin tallafi tare da kungiyar REDAID suka kai dauki wurin tun 14 ga Satumba.
Ya ce, marasa lafiya da cutar ba ta tsananta a jikinsu ba na karbar magani a ƙananan asibitoci, yayin da ake yi wa wadanda suka tsananta tiyata a manyan asibitoci.
Ya jaddada cewa wayar da kan jama’a na da muhimmanci, domin wasu mazauna yankin sun alakanta cutar da sihiri, abin da ya jinkirta neman magani da wuri.
Dr. Olufemi ya bayyana cewa Malabu gari ne mai nisa, da ke da tazarar awa biyu daga Yola, kuma rashin hanyoyi ya jinkirta isar da agaji cikin gaggawa.
Ya ce, tsaro na dogon lokaci kan kiwon lafiya ya shafi tsaftar ruwa da muhalli, domin jama’a za su rage zuwa koguna idan akwai rijiyoyin burtsatse da kuma na famfo.
Hukumar lafiya ta ƙasa ta tabbatar da cewa gwamnati tare da abokan hulɗa suna nan kan bakansu na kula da marasa lafiya da kuma hana yaɗuwar cutar.
No comments