Rundunar Sojin Sama ta Nijeriya (NAF) ta hannun tawagar Operating HADIN KAI (AC OPHD) ta yi nasarar kashe ‘yan ta’adda sama da 25 a wani sam...
Rundunar Sojin Sama ta Nijeriya (NAF) ta hannun tawagar Operating HADIN KAI (AC OPHD) ta yi nasarar kashe ‘yan ta’adda sama da 25 a wani samame na dare a Bula na jihar Yobe da Banki na Borno ranar 18 ga Satumba 2025.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da daraktan hulɗa da jama'a na rundunar, Ehimen Ejodame ya fitar a ranar Asabar.
A cewar sa, sojojin na Nijeriya sun kai farmakin ne na haɗin gwiwa a ranar 18 ga watan Satumba bayan samun bayanan sirri.
Ya ce, hakan ya sa suka yi amfani da fasahar zamani wajen ganowa da tattara bayanan zirga-zirgar mayaƙan, sannan suka far musu.
"Sojojin Nijeriya sun samu nasarar kashe aƙalla ’yan ta'adda guda 25 a wani farmakin haɗin gwiwa a yankin Bula na jihar Yobe da yankin Banki na jihar Borno a ranar 18 ga Satumba," inji shi.
No comments