Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

RAGE TSADAR KAYA: Gwamnatin Tarayya Ta Dakatar Da Harajin Kwastam Na Kashi 4% Kan Kayan Da Ake Shigo Da Su

  Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta dakatar da aiwatar da kuɗin harajin kashi 4% na Farashin kaya kafin ɗauko su daga ƙasar da aka samo...


 
Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta dakatar da aiwatar da kuɗin harajin kashi 4% na Farashin kaya kafin ɗauko su daga ƙasar da aka samo su ( Free on Board [FOB]) da Hukumar Kwastam ta sanya a kan kayan da ake shigo da su ƙasar nan.

A cikin wata sanarwa dabta fitar, Ma’aikatar Kuɗi ta bayyana cewa an ɗauki wannan mataki ne bayan dogon nazari da shawarwari daga masana harkar kasuwanci, masana tattalin arziki da kuma jami’an gwamnati.

A cewar Ma’aikatar, an gano cewa harajin na iya jefa ƙasar cikin ƙarin matsaloli na hauhawar farashi, tsadar kayayyaki, da kuma rage gasa a harkokin kasuwanci.

Wata sanarwa da Babban Sakataren Ma’aikatar Kuɗi, R. O. Omachi ya fitar, ta ce yawancin ’yan kasuwa da masu shigo da kaya sun nuna damuwa kan wannan haraji saboda nauyin da zai dora musu.

Sanarwar ta ce dakatarwar za ta ba da damar tattaunawa da sake nazari kan tsarin, tare da shirin samar da wata hanya mafi daidaito da za ta taimaka wajen tara kuɗaɗen shiga da kuma tabbatar da ci gaban tattalin arzikin ƙasa.

Ma’aikatar ta kuma umurci hukumomin da abin ya shafa da su tabbatar da bin wannan umarni kai tsaye.

No comments