Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

ShugabaTinubu Ya Yi Nuni Da Cewa Nijeriya Na Hanyar Kai Wa Ga Ƙarfin Tattalin Arziki Mai Ɗorewa

Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya ce tattalin arzikin ƙasar ya soma dawowa daidai sakamakon manufofin sauye-sauyen da gwamnatin sa ta aiwatar. S...


Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya ce tattalin arzikin ƙasar ya soma dawowa daidai sakamakon manufofin sauye-sauyen da gwamnatin sa ta aiwatar.

Shugaban ya bayyana haka ne a Ibadan, lokacin bikin naɗa Oba Rashidi Ladoja a matsayin Olubadan na 44 na Ibadanland. Kakakin Shugaban Ƙasa, Bayo Onanuga, ya ce Tinubu ya bayyana farin cikin sa da yadda ‘yan Nijeriya suka nuna haƙuri da goyon baya a lokacin aiwatar da manufofin.

“Ina farin cikin sanar da ku cewa tattalin arzikin mu ya soma gyaruwa, kuma yanzu akwai haske,” in ji Tinubu.

Shugaban ya kuma yaba da rawar da sabon Olubadan ya taka a tarihin siyasar Nijeriya, musamman yadda ya tsallake ƙoƙarin tsige shi daga kujerar gwamnan Jihar Oyo a baya. Ya bayyana shi a matsayin wata alama ta juriyar shugabanci da sadaukarwa ga jama’a.

A wajen bikin, Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, ya miƙa wa Oba Ladoja sandar iko da takardar shaidar zama Olubadan. Ya ce hakan ya kawo ƙarshen jayayya tsakanin dangin sarautar Ibadan.

A jawabin sa, sabon Olubadan ya bayyana naɗin nasa a matsayin hukuncin Allah, tare da gode wa shugaban ƙasa da gwamnan jihar bisa girmamawa da goyon baya.

Daga cikin manyan baƙi da suka halarci bikin akwai gwamnonin jihohin Ondo, Ekiti, da Osun, tsofaffin gwamnonin Cross River, Osun, Kano da Ogun, tare da shugabannin gargajiya ciki har da Sultan na Sokoto, Alaafin na Oyo da Soun na Ogbomoso.




 

No comments