Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

JIHAR KADUNA: Ɗalibai 32,000 Ne Za Su Rinƙa Samun Horo A Sana’o'in Hannu Daban-davan A Duk Shekara

Gwamnatin Jihar Kaduna, ƙarƙashin jagorancin Gwamna Uba Sani, ta sanar da shirin ta na horas da ɗalibai  32,000  a duk shekara ta hannun Cib...


Gwamnatin Jihar Kaduna, ƙarƙashin jagorancin Gwamna Uba Sani, ta sanar da shirin ta na horas da ɗalibai  32,000  a duk shekara ta hannun Cibiyar Horas da Sana’o’i da Ƙwarewa da aka kafa a kwanan nan.

Cibiyar, wacce Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ƙaddamar a watan Yuni, tana da rassan da aka tsara su da kyau a Rigachikun, Soba da Samarun Kataf. Rassan cibiyar sun samu kayan aiki na zamani domin samar da horo na dindindin, wanda zai ba da ƙwarewa ta zahiri da ta zamani da kuma ta duniya.

Ɗalibai na iya yin rajista a cikin kowanne daga cikin fannoni 14 na sana’o’in da Hukumar Kula da Ilimin Fasaha ta Ƙasa (NBTE) ta amince da su, waɗanda suka haɗa da: Fenti da Kwalliya (POP/, Gini da Sanya Tiles da Bututun Ruwa (Plumbing), Kere-kere da Gyaran Katako Walda da Kera Karfe daq  Sanya Wutar Lantarki da Kera Aluminium da  Firiji da A/C da kuma Sanya Hasken Rana sai kuma Gyaran Kwamfuta , Girki da Kulawa da Baƙi  da Ƙira da Dinkin Kaya.

Yayin da yake bayani kan muhimmancin wannan shiri, Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Kaduna, Malam Ahmed Maiyaki, ya ce: “Wannan Cibiyar wata gagarumar alama ce ta kudurin Gwamnatin Jihar Kaduna na bunkasa koyon sana’o’i, karfafa matasa, da haɓaka tattalin arziki. 

Ya ce, "an zaɓi fannonin sana’o’i 14 ne cikin hikima domin su magance manyan bukatun ƙwararrun ma’aikata a bangarorin gine-gine, makamashi, fasahar zamani (ICT), kula da baƙi, da harkokin ƙirƙira.

"Muna da yaƙinin cewa waɗanda suka kammala karatu a wannan Cibiyar ba kawai za su samu ayyukan yi ba ne, har ma za su zama masu dogaro da kai kuma su samar da dama ga wasu.”

Shi ma  Shugaban Cibiyar, Malam Husaini Haruna Muhammad, ya jaddada muhimmancin da horon ke da shi wajen dacewa da bukatun kasuwanni da wuraren aiki: “Abin da muke mayar da hankali a kai shi ne samar da daliban da suka kammala karatu waɗanda suke da shirye-shiryen fuskantar kasuwa da wuraren aiki.

"Kashi 80% na horon mu yana kasancewa ne na aikace-aikace, wanda ke ba wa ɗalibai damar samun ƙwarewar rayuwa ta ainihi a fannonin da suka zaɓa. Wadannan ƙwarewar ba wai kawai sun dace da tattalin arzikin Nijeriya ba ne, har ma suna da gasa a matakin duniya.

"Muna ƙarfafa 'yan ƙasa musamman mata, masu nakasa da matasa masu rauni  da su amfana da wannan dama.”

Tare da kayan aiki da ma'aikata masu ƙwarewa da aka tanada, cibiyar na da niyyar yaye ɗalibai 16,000 a zangon horo na farko, tare da nufin cimma burinta na yaye ɗalibai 32,000 a kowace shekara.

Ya ce, Gwamnatin Jihar Kaduna na kira ga al’ummar jihar da ma wajenta da su yi amfani da wannan dama don samun ƙwarewa da za ta basu damar samun aiki, kafa nasu sana’a, da dogaro da kai.
 

No comments