Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Gwamnatin Jihar Kaduna Ta Nemi Al'umma Su Himmatu Wajen Rajistar Katin Zabe

Gwamnatin Jihar Kaduna ta nuna damuwa kan ƙarancin masu zuwa yin rajistar katin jefa ƙuri’a a cikin aikin rajistar da ake yi a halin yanzu, ...

Gwamnatin Jihar Kaduna ta nuna damuwa kan ƙarancin masu zuwa yin rajistar katin jefa ƙuri’a a cikin aikin rajistar da ake yi a halin yanzu, tana roƙon shugabannin Ƙananan Hukumomi, Sarakunan gargajiya, shugabannin addini, da ‘yan jarida su ƙara himma wajen wayar da kan jama’a.

Kwamishinan Harkokin Yaɗa Labarai, Malam Ahmed Maiyaki, ya bayyana cewa Gwamna Uba Sani, a matsayin shugaba mai kishin Dimokraɗiyya da haɗin kai, ya ɗauki matakan da suka dace don tabbatar da ƙara yawan masu rajista domin samun halartar jama’a.

Maiyaki ya bayyana wannan damuwa ne a jawabin da ya gabatarwa wqjen taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar domin nazarin matsalolin da aikin ke fuskanta da kuma tsara dabaru don ƙara yawan masu rajista.

A cewar sa, rahotannin farko daga Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) sun nuna cewa Jihar Kaduna da Arewa maso Yamma na baya a yawan masu rajista, lamarin da ya jawo hankalin Gwamnatin Tarayya.

Ya bayyana cewa an faɗaɗa taron ne da gangan don haɗa shugabannin Ƙananan Hukumomi, slSarakuna, shugabannin addini, da ‘yan jarida saboda muhimmancin rawar da suke takawa wajen wayar da kan jama’a daga sassa daban-daban.

“Gwamnati na matuƙar damuwa wajen tabbatar da ƙarin shiga cikin wannan aikin daga al’umma. Wannan ba game da son ɓangare ba ne; yana game da ƙarfafa dukkan ɓangarorin al’umma Kama daga matasa, mata, manya, da kowane rukuni na jinsi su shiga cikin tsarin dimokiradiyya,” in ji Maiyaki.

Kwamishinan ya yaba wa wasu shugabannin ƙananan hukumomi da suka riga suka fara gudanar da kamfen ɗin wayar da kai a yankunansu, yana mai cewa taron ya samar da dandali na musayar ƙwarewa da tsara haɗin gwiwa don cimma babban tasiri.
 

No comments