Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Farashin Kayan Masarufi Na Ci Gaba Da Sauka A Nijeriya - Hukumar Ƙididdiga Ta Ƙasa (NBS)

Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS) ta ce farashin kaya a Nijeriya ya sauka zuwa kashi 20.12 cikin ɗari a watan Agusta 2025. A cikin rahoton da ...

Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS) ta ce farashin kaya a Nijeriya ya sauka zuwa kashi 20.12 cikin ɗari a watan Agusta 2025.

A cikin rahoton da hukumar ta fitar kan Consumer Price Index (CPI) da hauhawar farashin kaya na watan Agusta, ta bayyana cewa adadin ya ragu da kashi 1.76 cikin ɗari idan aka kwatanta da na watan Yuli wanda ya kai kashi 21.88 cikin ɗari.

Hukumar ta ce idan aka yi la’akari da shekara ɗaya kacal, hauhawar farashin kaya ya yi ƙasa da kusan kashi 12.03 cikin ɗari, inda a watan Agusta 2024 aka samu kashi 32.15 cikin ɗari.

Rahoton ya kuma nuna cewa, hauhawar farashin abinci ya tsaya a kashi 21.87 cikin ɗari idan aka kwatanta da bara, inda ya kai kashi 37.52 cikin ɗari.

A matakin wata zuwa wata kuwa, farashin abinci ya tsaya a 1.65 cikin ɗari, bayan da a watan Yuli ya kai 3.12 cikin ɗari.

A cikin rahoton, an bayyana cewa hauhawar farashi a birane ya tsaya a 19.75 cikin ɗari, yayin da a karkara ya kai 20.28 cikin ɗari.

Rahoton ya kawo jerin jihohin da suka fi samun hauhawar farashi a shekara wanda suma haɗa da:
    •    Ekiti (28.17%)
    •    Kano (27.27%)
    •    Oyo (26.58%)

Jihohin da suka fi samun saukin hauhawar farashi kuwa sun haɗa da:
    •    Zamfara (11.82%)
    •    Anambra (14.16%)
    •    Enugu (14.20%)

A bangaren abinci kuwa, rahoton ya ce jihohin da suka fi hauhawar farashi a shekara sun haɗa da:
    •    Borno (36.67%)
    •    Kano (30.44%)
    •    Akwa Ibom (29.85%)

Yayin da Zamfara (3.20%), Yobe (3.60%) da Sokoto (6.34%) suka fi samun sauƙi.
 

No comments