Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya kammala hutunsa na aiki a waje tun kafin lokacin da aka tsara, inda ake sa ran zai dawo Abuja gobe Talata, 1...
Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya kammala hutunsa na aiki a waje tun kafin lokacin da aka tsara, inda ake sa ran zai dawo Abuja gobe Talata, 16 ga Satumba, 2025 domin ci gaba da aiki.
Shugaban ya tafi Faransa ne tun ranar 4 ga Satumba domin yin wani ɓangare na hutun shekara, inda a baya aka shirya ya raba lokacin hutun tsakanin Faransa da Birtaniya.
A makon jiya a Paris, Shugaba Tinubu ya gana da takwaransa na Faransa, Emmanuel Macron, a wata liyafa a fadar Élysée. Shugabannin biyu sun tattauna kan muhimman fannoni na haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen su, tare da amincewa wajen ƙara zurfafa dangantaka domin ci gaban tattalin arziki da zaman lafiya a duniya.
Mai ba shugaban ƙasa shawara na musamman kan harkokin bayani da dabarun sadarwa, Bayo Onanuga, ne ya tabbatar da dawowar shugaban a cikin wata sanarwa da ya fitar yau Litinin.
No comments