Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Masu Wulaƙanta Naira Ke Ƙara Haifar Da Tsadar Buga Sabbin Kuɗi -CBN

Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya bayyana cewa masu wulaƙanta takardun naira ne ke haddasa yawan hauhawar tsadar buga sabbin kuɗi a Nijeriya. ...

Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya bayyana cewa masu wulaƙanta takardun naira ne ke haddasa yawan hauhawar tsadar buga sabbin kuɗi a Nijeriya.

Wannan jan-kunne ya fito ne daga bakin Mataimakin Gwamnan CBN, da ke Sashen Ayyukan Yau da Kullum, Bala Bello, yayin da yake jawabi wurin rangadin wayar da kan jama'a dangane da yadda za a riƙa tu'ammali da takardun naira, ba tare da an yagalgala kuɗaɗen ba.

Rangadin wayar da kan wanda aka ƙaddamar a Abuja, ya samu wakilci daga Daraktan Hada-hadar Kuɗaɗe Dakta Sikiru Adetona, wanda ya ƙara da cewa wulaƙanta naira ta hanyar shafa mata datti, duƙunƙune ta ko kekketa ta da yagalgala ta yayin hada-hadar kuɗaɗe, yana rage mata martaba da karsashin daraja.

"Idan ba mu tashi tsaye mun kawar da wannan matsalar ba, to masu wulaƙanta takardun kuɗaɗe za su ci gaba da haddasa tsadar buga sabbin kuɗaɗen da za a maye gurbin waɗanda aka lalata da su."

Bello ya ce darajar naira ta wuce matsayin takardar kuɗin da ake biyan ciniki ko hada-hada da ita. Ya ce naira abin alfahari ce ga Nijeriya, tauraruwar da ke haskaka ƙasar nan.

"Amma abin takaici sai ka riƙa ganin wasu ba su riƙe ta da daraja, suna duƙunƙune ta, su kekketa ta, wasu su riƙa liƙi suna watsa naira a wuraren bukukuwa, wasu su riƙa rubutu kan ta, wasu ma su shafa mata datti, su yagalgala ta, ko su cumuimuye ta.

Ya ce ƙoƙarin da ake yi don kare darajar Naira ba a kan wuyan CBN kaɗai ya rataya ba, amma har da ɗaukacin 'yan Nijeriya baki ɗaya duk nauyin ya rataya a wuyan su.

Ya ce a wannan ƙoƙarin cusa wa jama'a kare ƙimar naira da daina wulaƙanta ta, akwai buƙatar haɗin-gwiwa tsakanin masu ruwa da tsaki a ɓangaren hada-hadar kuɗaɗe, ciki har da bankunan kasuwanci, ƙananan bankunan hada-hada, ƙungiyoyin sufurin motoci, ƙungiyoyin 'yan kasuwa, shugabannin kasuwanni, ƙungiyoyin addini, ƙungiyoyi masu zaman kansu da kuma kafafen yaɗa labarai.

Ya yi kira ga: "Masu kasuwanci da 'yan tireda da masu motocin haya su taimaka wajen daina wulaƙanta kuɗi. Kungiyoyin jama'a da kafafen yaɗa labarai su ma su yayata wannan kamfe ya isa gida-gida, yayin da sauran dukkan 'yan Nijeriya tilas su zama dakarun kare daraja da ƙimar naira. Ta haka ne za a samu nasarar canja ɗabi'ar mutane su riƙa riƙe takardun kuɗi da daraja."

Yayin da bukukuwan Kirsimeti da ƙarshen shekara ke gabatowa, Bello ya gargaɗin cewa kada a riƙa ɓoye kuɗi ana kimshe su, domin yin hakan na hana wasu samun isassun kuɗaɗen da za su riƙa hada-hada, kuma yana kawo cikas da naƙasun ƙarancin kuɗaɗen da ke hannun jama'a."

Ya bayyana cewa wannan shirin rangadin wayar da kai don hana jama'a wulaƙanta takardun kuɗaɗe, zai karaɗe jihohin ƙasar nan da ƙananan hukumomi, har ma da wasu yankunan karkara.

Shi kuwa Adetona a nasa jawabin, ya tabbatar da cewa  CBN zai samar da wadatattun kuɗaɗen hada-hada a lokacin Kirsimeti da hutun ƙarshen shekara. Sai dai ya yi kira da a ci gaba da riƙe su da daraja.

Ita ma Daraktar Hulɗa da Jama'a ta CBN, Hakama Sidi Ali, ta ce duk da yake haƙƙin CBN ne ya samar da takardun naira, kuma ya tabbatar wadatattun kuɗaɗe masu tsafta, to kuma ta ce haƙƙi ne mai nauyi kan kowane ɗan Nijeriya ya riƙa daratta naira, ta hanyar daina wulaƙanta ta, ya tsaftace ta kuma ya daina yagalgala ta.

Ta ce takardun naira masu tsafta sun fi kwarjini a ido da ƙima yayin hada-hada.

No comments