Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

NAPTIP Ta Ceto Yara Takwas Da Aka Sace Daga Arewacin Nijeriya

Jami'an Hukumar Hana Fasa Ƙaurin Jama'a ta Nijeriya (NAPTIP) ta kuɓutar da wasu ƙananna yara takwas da ake zargin an sace su daga wa...



Jami'an Hukumar Hana Fasa Ƙaurin Jama'a ta Nijeriya (NAPTIP) ta kuɓutar da wasu ƙananna yara takwas da ake zargin an sace su daga wani gidan marayu a Kano da wasu jihohin arewacin ƙasar.

Cikin wata sanarwa da jami'in hulda da jama'a a hukumar, Vincent Adekoye ya fitar ranar Talata ya ce an yi safarar yaran ne zuwa yankunan kudu maso kudanci, da kudu maso gabashin ƙasar amma aka kuɓutar da su a jihar Delta.

“Bayan samamen da muka kai gidan marayun Delta, mun gano cewa akwai ƙananan yara fiye da 70 a cikin gidan marayu, ciki har da jarirai 15, daga nan muka gano cewa takwas daga ciki akwai zargin cewa daga Kano aka kawosu, daga nan muka kuɓutar da su,'' inji sanarwar.

Sanarwar ta ce tuni aka mayar da yaran da aka gano zuwa Kano, inda tuni aka gano su tare da sada su da danginsu.

Batun satar ƙananan yara musamman a Arewacin Nijeriya, wata matsala ce da take ci gaba da addabar ƙasar, inda a wasu lokuta ake sayar da su.

No comments