Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya sake taso gwamnatin Bola Tinubu a gaba. Atiku ya bayyana cewa sama da shekaru biyu da Sh...
Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya sake taso gwamnatin Bola Tinubu a gaba.
Atiku ya bayyana cewa sama da shekaru biyu da Shugaba Tinubu ya karbi ragamar mulki, babu wata alamar cewa zai iya magance yunwa da talaucin da su ka addabi ƙasar nan.
Hakan na ƙunshe a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun bakinsa, Paul Ibe, ya fitar.
Jagoran 'yan adawan ya bayyana yunwar da ake fama da ita a ƙasar nan a matsayin abin da ba za a amince da shi ba, musamman ma ga matalauta da marasa galihu.
"Duk mafi munin tarzoma da juyin juya halin siyasa da zamantakewa a duniya an fi hura wutarsu ne saboda mummunar yunwa da rashin kayan more rayuwa," inji Atiku.
Atiku ya ce, babban aikin kowace gwamnati shi ne kare rayuka da samar da walwala ga jama’a, amma talakawan Nijeriya na ci gaba da nutsewa cikin baƙin talauci a qarqashin mulkin Shugaba Tinubu da jam’iyyar APC.
Atiku ya yi gargaɗin cewa halin da ake ciki yanzu ba abin murna ba ne, domin yana ƙara haifar da matsaloli na aikata laifuffuka kamar zamba, ta’addanci, garkuwa da mutane, shiga ƙungiyoyin asiri, shaye-shaye.
“A nan gida Nijeriya, ba zai zama abin mamaki ba idan aka ce ma har zanga-zangar EndSARS ta samo asali ne daga takaicin yunwa da rashin kulawar gwamnati ga jama’a.”
Atiku ya ƙara da cewa, duk da iƙirarin sauye-sauyen da gwamnatin Tinubu ke cewa tana yi, haqiqanin magana ita ce rashin tabbas kan abinci ya zama ruwan dare a faɗin ƙasar nan.
"Babu wata gwamnati mai daraja da ba ta sanya walwala da tsaron jama’a a matsayin babban ginshiƙin ta ba," inji Atiku.
Ya jaddada cewa tunda ana yin sauye-sauye ne don al’umma, ba don gwamnati ba, to dole a yi irin waɗannan sauye-sauyen tare da yin la’akari da halin da mutane za su shiga.
Ya ce, "ko da kuwa waxanda ke kan mulki a yanzu sun amince ko ba su amince ba, gaskiyar rayuwarmu ita ce matalauta na kara mutuwa saboda yunwa, yayin da mafi yawan waɗanda ke raye su ke fama da manufofin wannan gwamnati marasa inganci."
No comments