Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Nan Ba Da Jimawa Ba Za A Daina Ɗauke Wuta - Gwamnatin Tarayya

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa Nijeriya ta kamo hanyar zuwa matakin samar da wutar lantarkin da ba za a riƙa ɗaukewa ba. Ministan Wutar L...



Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa Nijeriya ta kamo hanyar zuwa matakin samar da wutar lantarkin da ba za a riƙa ɗaukewa ba.

Ministan Wutar Lantarki, Adebayo Adelabu, ne ya bayyana haka a Abuja yayin ƙaddamar da wasu ayyuka a Cibiyar Horar da Ma’aikatan Wutar Lantarki ta Nijeriya (NAPTIN).

Daga cikin ayyukan da aka qaddamar a NAPTIN akwai ɗakunan horarwa guda biyar da gidan kwanan ɗalibai mai ɗakuna 104.

Adelabu ya ce, wannan sababbin gine-gine sun shiga tarihi a cibiyar kuma za su taimaka wajen ƙara inganta bangaren makamashi a Nijeriya
Nijeriya za ta samar da wuta mara yankewa

A cewarsa, wannan aiki da aka kammala ya ƙara tabbatar da cewa gwamnatin Shugaba Tinubu mai faɗa da cikawa ce, tana aiwatar da abin da ta yi alƙawari.

Ministan ya ce, ƙoƙarin da Gwamnatin Tarayya ke yi ya fara haifar da sakamako mai kyau domin wutar lantarki da ake samarwa yanzu ta zarce ta baya.

"Nan ba da jimawa, za a samar sa wutar lantarki babu yankewa, za daina ɗauke wuta a tsawon awanni 24 na kowace ranar mako. Wannan abu ne da zai yiwu kuma mun fara ganin alamu."

Ministan ya ce, fwamnati na samar da hasken wutar lantarki a jami’o’i, asibitocin koyarwa, cibiyoyin kiwon lafiya, hukumomin gwamnati da garuruwa.

Adebayo Adelabu ya jaddada cewa wuta ita ce ginshiqi ga ci gaban sauran muhimman sassan tattalin arziki kamar ilimi, lafiya da sufurin jiragen sama.

“Muna da duk abin da ake buqata domin fara ƙera na’urorin auna wuta, wayoyi, tiransufoma, da manyan batura a nan cikin gida, za a yi gagayya da mu a duniya nan gaba.

"Muna da kwakwalwa, muna da mutane masu hazaka, dole mu dogara da kanmu, kuma muna dab da cimma hakan," inji minista Adelabu.

Adelabu ya ce, sababbin wuraren horaswar da aka gina sun tabbatar da qudirin gwamnati na samar da kwararrun ma’aikata da za su iya shawo kan ƙalubale a bangaren makamashi.

Shugaban NAPTIN, Ahmed Nagode, ya bayyana cewa wannan aikin wani tubali ne da zai haskaka makomar bangaren wutar lantarki a Nijeriya.

Ya ce, cibiyar na da shirin ƙulla haxin gwiwa domin aiwatar da shirin Next Generation Rescue Programme da zai horar da matasan Nijeriya tare da ba su dama.

No comments