Hukumar Kwastan ta Nijeriya (NCS) ta bayyana cewa ta karɓi umarnin Ma’aikatar Kuɗi na dakatar da aiwatar da harajin kashi 4% na Farashin kay...
Hukumar Kwastan ta Nijeriya (NCS) ta bayyana cewa ta karɓi umarnin Ma’aikatar Kuɗi na dakatar da aiwatar da harajin kashi 4% na Farashin kaya kafin ɗauko su daga ƙasar da aka samo su wato Free-on-Board (FOB) da aka ɗora kan kayan da ake shigo da su ƙasar nan.
A cikin wata sanarwa da Kakakin hukumar, Dr Abdullahi Maiwada, ya fitar a ranar Litinin, hukumar ta ce tana godiya da wannan matakin da Ma’aikatar Kuɗi ta ɗauka tare da tabbatar da cewa za ta ci gaba da bin manufofin gwamnati na tattalin arziƙi.
Dr Maiwada ya ce hukumar ta fara tattaunawa da Ma’aikatar Kuɗi domin tabbatar da cewa ba a samu cikas a ayyukan hukumar ba.
Hukumar ta kuma yi ƙarin haske kan rahotannin da ke yaɗuwa a kafafen yaɗa labarai cewa harajin kashi 4% na FOB ƙirƙiro shi a kayi a ‘yan kwanakin nan.
Ta ce wannan tanadi ne na doka da Majalisar Tarayya ta kafa a cikin Sashe na 18(1)(a) na Dokar Hukumar Kwastan ta 2023, wanda ya tanadi cewa “ba za a karɓi ƙasa da kashi 4% na FOB ba akan kayan da ake shigo da su, bisa tsarin da duniya ke bi.”
Hukumar ta tabbatar da cewa za ta ci gaba da gudanar da ayyukanta yadda ya kamata ba tare da tangarɗa ba, tare da tabbatar da sauƙaƙe cinikayya da kuma ƙara samun kudaden shiga ga gwamnati.
“Muna da ƙwarin gwiwa cewa tattaunawa da Ma’aikatar Kuɗi da sauran masu ruwa da tsaki za su samar da mafita da za ta fi amfani ga Nijeriya baki ɗaya, ta hanyar ƙara samun kuɗaɗen shiga da bunƙasa tattalin arziƙin ƙasa,” in ji sanarwar.
Hukumar Kwastan ta ce za ta ci gaba da aiki da ‘yan kasuwa, masu fitar da kaya da hukumomin ƙasa da ƙasa wajen tabbatar da gudanar da ayyuka cikin bin ƙa’idoji.
No comments