Wata kotun sojoji a jihar Filato ta yanke wa sojan Nijeriya hukuncin rataya bayan kama shi da laifin kisan wani matashi. Ana tuhumar sojan d...
Wata kotun sojoji a jihar Filato ta yanke wa sojan Nijeriya hukuncin rataya bayan kama shi da laifin kisan wani matashi.
Ana tuhumar sojan da hallaka wani mutum mai tuka Keke Napep a Azare da ke jihar Bauchi a Arewacin Nijeriya.
Kotun ta yanke wa Lukman Musa hukunci bayan ta same shi da laifin kisa, haÉ—in baki da mallakar harsashi ba bisa Æ™a’ida ba, Æ™arÆ™ashin jagorancin Birgediya Janar Liafis Bello.
A shari’ar, kotun ta ce, Musa da abokin sa Oba sun jawo Isa cikin gidan sa da sunan taimaka masa, sai suka buge shi sannan suka shake shi.
Domin boye laifin sa, Musa ya saka gawar mai Keke Napep a cikin jaka, ya yar a tsakanin ƙauyen Shira da Yala, inda daga baya aka sayar da Keken.
Kotun ta kuma kama Musa da mallakar harsai guda 34 na 7.62mm ba tare da izini ba, lamarin da ya ƙara nauyin tuhume-tuhumen sa.
Yayin yanke hukunci, Janar Bello ya bayyana aikin sa da cewa “wauta ce da rashin imani,” yana mai cewa ya saba wa dokokin soja da amana ga jama’a.
Ya ce, “Ka canza daga mai kare jama’a zuwa mai kashewa. Aikin ka abin kunya ne ga sojojin Nijeriya."
An yanke masa hukuncin kisa bisa dokar 'Penal Code' sashe na 220, yayin da aka kuma yanke masa shekara biyu a kurkuku bisa mallakar harsashi.
Haka kuma kotun ta kori Musa daga aikin soja tare da bayyana shi a matsayin wanda ya saba wa tsarin aiki da na doka.
Mai ba da shawara na shari’a na rundunar, Manjo Aminu Mairuwa, ya ce wannan hukunci na nuna jajircewar rundunar wajen tabbatar da doka da ladabi.
“Wannan hukunci alama ce cewa rundunar soja ba za ta bari wani jami’i ya yi watsi da doka ko tsarin aiki ba," in ji Aminu Mairuwa.
No comments