Ashafa Murnai Barkiya Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Olayemi Cardoso, ya yi kakkausan gargaɗi ga masu wulaƙanta takardun Naira, waɗa...
Ashafa Murnai Barkiya
Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Olayemi Cardoso, ya yi kakkausan gargaɗi ga masu wulaƙanta takardun Naira, waɗanda suka ƙunshi watsa takardun Naira yayin bukukuwa, masu duƙunƙune takardun kuɗaɗen, masu hada-hadar sabbin kuɗi da kuma masu buga kuɗaɗen jabu.
Wannan gargaɗi ya fito ne ta bakin Kakakin Babban Bankin, Hakama Sidi Ali, wadda ta wakilci Cardoso a wani taron wayar da kan jama'a da Babban Bankin Nijeriya ya shirya a ranar Alhamis, a Kaduna.
Ya ce dukkan waɗannan laifuka ne masu nuna rashin kishin ƙasa, kasancewa wulaƙanta Naira tamkar wulaƙanta ƙasa ce ɗungurugum.
Taron wanda CBN ya raɗa wa suna "Samar da Hanyoyin Hada-hadar Kuɗaɗe a Matsayin Dabarun Bunƙasa Tattalin Arziki," an shirya shi ne kacokan domin ƙarfafa wa jama'a yadda za su gane tare da fahimtar tsare-tsaren Babban Bankin Najeriya, sai kuma rawar da al'umma za su taka wajen samar wa tattalin arziki nagartattun ƙafafun da zai iya tsayuwa a kai.
Cardoso ya ce an bijiro da wannan shiri domin fito da kusanci tsakanin muhimmancin amfani da asusun banki da kuma bunƙasa Ƙanana da Matsakaitan Masana'antu (SMEs), waɗanda ke da muhimmin tasiri wajen saisaita daidaiton farashi da kuma inganta tattalin arziki.
"Ina gargaɗin kowa cewa ya riƙe Naira da daraja sosai, ya daina sa mata datti. A guji watsa takardun Naira yayin tarukan bukukuwa da shagulgula. A daina hada-hadar sabbin nairori, a daina duƙunƙune Naira, kuma a daina buga jabun kuɗaɗe. Saboda Naira ita ce alamar ƙima da darajar Najeriya.
Gwamnan CBN ta bakin Hakama Ali ya ce taron yana daga shirin da bankin ya bijiro da shi, domin ci gaba da bayyana wa jama'a irin tasirin da yake sanarwa wajen inganta rayuwar su, bunƙasa tattalin arziki da ciyar da harkokin kasuwancin su gaba.
Ya ci gaba da cewa an fara ganin alfanun sabbin tsare-tsaren da CBN ya fito da su, kamar samun ƙarin masu zuba jari a Najeriya, cinikayya mai riba ba mai giɓin hada-hadar kuɗaɗe ba, sai kuma ƙarin masu amfani da asusun banki wurin hada-hadar su.
Cardoso ya lissafa manyan nasarorin da CBN ya samar, waɗanda ya ce sun haɗa samar farashin musayar Naira da kuɗaɗen waje na bai-ɗaya, kawar da matsalar musayar kuɗaɗen waje na Dala biliyan 7, bayan an tantance, sai kuma ci gaba da ake kan yi wajen ƙarfafa jarin bankuna, da nufin cimma ƙudirin ganin darajar tattalin arzikin cikin gida na Najeriya ya kai Dala tiriliyan ɗaya.
No comments