Tsohon mataimakin shugaban Nijeriya kuma jagoran adawa Atiku Abubakar ya ɗauki nauyin karatun ɗalibai uku da suka yi nasara a gasar Turancin...
Tsohon mataimakin shugaban Nijeriya kuma jagoran adawa Atiku Abubakar ya ɗauki nauyin karatun ɗalibai uku da suka yi nasara a gasar Turancin Ingilishi ta TeenEagle Global Finals a Ingila.
Wata sanarwa da Gidauniyar Atiku ta fitar mai kwanan watan 5 ga watan Agusta ta ce nasarar da Nafisa Abdullahi, da Rukaiya Mohammed Fema, da Khadija Kashim Kalli suka yi "shaida ce cewa kwane yaro na iya cim ma burika".
"Saboda karrama wannan bajinta taku, Gidauniyar Atiku Abubakar za ta ɗauki nauyin kammala karatun sakandare da kuma na duk jami'ar da kuka zaɓa," a cewar sanarwar da sakataren gidauniyar, Farfesa Ahmadu Shehu ya fitar.
A farkon watan Agusta ne matasan 'yan asalin jihar Yobe suka doke takwarorinsu 20,000 daga sassan duniya a gasar bayan sun wakilci Najeriya daga makarantar Tulip International College.
Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafukan sada zumunta, Atiku ya ce a jiya Alhamis ne ɗaya daga cikinsu Nafisa Abdullahi ta kai masa ziyara a gidansa da ke Abuja, babban birnin Nijeriya.
No comments