Hukumomi a jihar Bauchi da ke arewacin Nijeriya sun tabbatar da mutuwar mutum 58 sakamakon annobar amai da gudawa a ƙananan hukumomi 14 ciki...

Haka nan, akwai mutum 258 da aka tabbatar sun kamu da cutar ta kwalara, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito Mataimakin Gwamnan Bauchi Auwal Mohammed Jatau yana bayyanawa ranar Alhamis.
Babban jami'in gwamnatin ya bayyana hakan ne yayin rantsar da wasu kwamatoci biyu domin yaƙi da kwalara.
"Wannan annobar abu ne da za a iya magancewa a tsawon lokaci ta hanyar tsaftace ruwan sha, da tsaftar jiki," inji shi.
No comments