Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya ƙaddamar da wani sabon shiri da ake kira RenewHER, wanda manufar sa ita ce inganta lafiyar mata, musamman ...
Shugaba
Bola Ahmed Tinubu, ya ƙaddamar da wani sabon shiri da ake kira
RenewHER, wanda manufar sa ita ce inganta lafiyar mata, musamman masu
juna biyu, da kuma rage mace-macen mata awajen haihuwa a Nijeriya.
An gudanar da taron ƙaddamar da shirin ne a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja, inda Mataimakin Shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya wakilci shugaba Tinubu.
A jawabin sa, Shugaba Tinubu ya ce lafiyar mata ita ce ginshiƙin ci gaban kowace al’umma, don haka shirin zai kasance ginshiƙin haɗa kai tsakanin gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki wajen bunƙasa kiwon lafiya a ƙasar.
Shirin RenewHER zai samar da ofishi na musamman na shugaban ƙasa kan lafiyar mata, wanda zai yi aiki tare da ma’aikatun lafiya da harkokin mata, da kuma ƙungiyar matan gwamnoni, domin tabbatar da cewa an shigar da lafiyar mata cikin manufofin gwamnati a kowane mataki, daga jiha har zuwa Ƙananan Hukumomi.
Bugu da ƙari, an sanar da kafa dandalin yanar gizo na lafiyar mata mai amfani da fasahar AI, wanda zai taimaka wajen yada bayanai kan lafiyar iyaye mata da ’yan mata, kariya daga cututtuka, da kuma shirye-shiryen kiwon lafiya da ake bukata a sassa daban-daban na ƙasar.
A nata jawabin, matar gwamnan Jihar Kwara wacce kuma ita ce shugabar ƙungiyar matan gwamnoni, Farfesa Olufolake AbdulRazaq, ta ce RenewHER alama ce ta jajircewar gwamnatin Tinubu wajen inganta rayuwar mata da ƙarfafa musu gwiwa.
Ita ma mai bai wa shugaban ƙasa shawara ta musamman kan lafiyar mata, Dakta Adanna Steinacker, ta ce shirin RenewHER ya samo asali ne daga hangen nesa na Shugaba Tinubu na daukar lafiyar mata a matsayin muhimmin al’amari na kasa.
Haka kuma, wakiliyar Kungiyar Matan Majalisar Dinkin Duniya (UN Women) a Najeriya, Beatrice Eyong, ta bayyana shirin a matsayin “wani sauyi” kuma karo na farko da gwamnatin Najeriya ta dauki irin wannan mataki a matakin shugabanci mafi girma.
Taron ya samu halartar manyan jami’an gwamnati da matan gwamnoni da kuma jakadu.

No comments