Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Masarautar Zuru Ta Fitar Da Tsarin Yadda Za A Rinƙa Ambatar Sarautar Zuru

 Masautar Zuru da ke jihar Kebbi ta fitar da wani tsari, ko yanayin da ta ke so a rinƙa kira, ko ambatar Sarkin na Zuru, inda ta bayyana cew...


 Masautar Zuru da ke jihar Kebbi ta fitar da wani tsari, ko yanayin da ta ke so a rinƙa kira, ko ambatar Sarkin na Zuru, inda ta bayyana cewa za rinƙa kiran Sarautar da 'Mai Martaba Muhammadu Sanusi Mika'ilu (Sami Gomo III), Sarkin Zuru.

Wannan yana ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Sakataren Masarautar, Alhaji Muhammad Yahaya Marafa ya sanya wa hannu, inda ya ce, "Wannan suna da masarautar ta fitar, zai nuna ci gaba da tabbatar da kyawawan al'adu, tare da nuna tsarin Sarautar Zuru."

Sanarwar ta ce, da wannan yanayin sunan ne za a rinƙa jingina su da shi, ta hanyar gargajiya, shi ne aka amince da shi a masarautar, da shi ne kuma za a rinƙa yi wa Sarkin inkiya.

Daga nan sanarwar ta bayyana cewa Mai Martaba yana nuna matuƙar jin daɗin sa ga 'ya'yan Zuru, masoya da abokan arziki bisa irin goyon baya da addu'o'in da suke yi wa Masarautar.
 

No comments