Al'ummar garin Magama Gumau da ke Ƙaramar Hukumar Toro da jihar Bauchi suna cikin jimami da tusayawa ga wata yarinya 'yar kishiya, m...
Al'ummar garin Magama Gumau da ke Ƙaramar Hukumar Toro da jihar Bauchi suna cikin jimami da tusayawa ga wata yarinya 'yar kishiya, mai kimanin shekaru biyar, wacce mariƙiyarta ke azabtar da ita da wuta sakamakon fitsarin kwance.
Yarinyar, wacce mahaifiyarta ta rasu kimanin shekara ɗaya da ta gabata, tana tare da mahaifin ta ne mai suna Muhammad Umar, da ɗaya matar tasa, Rabi Nuhu, inda maƙwabtan su suka bayyana cewa yarinyar tana zama cikin azaba da masifa.
Rahotanni sun cewa wannan yarinya ta yi fama da baƙar azaba, inda ta ke shan duka kullu yaumin, mafi munin azabar ma, ita ce yadda matar ke azabatar da yarinyar da wuta, inda bayan ƙuna a jiki, jlhar farjin ta.
Da wannan ƙaramar yarin ta gaji da wannan baƙar azaba ne, sai ta shaida ma kawunta, inda ta roƙe shi ya ba ta katifa, ta shaida masa cewa kishiyar mahaifiyar ta tana sanya mata wuta a farji, kawai don ta yi fitsarin kwance. Wannan ne ta sa kawun nata ya kai rahoto a ofishin 'yan sanda na Toro.
A nasa bangaren, mahaifin yarinyar, Umar ya bayyana cewa matar tasa ta yaudare shi a lokacin da ya ga wata ƙuna a jikin yarinyar, inda matar ta ce wai ruwan shayi ne ya ƙona ta, "kuma har na yarda da ita. Ban fahimci gaskiyar lamarin ba, sai yanzu da asiri ya tonu," in ji shi.
Mai magana da yawun 'yan sandan jihar Bauchi, CSP Mohammed Wakil, ya tabbatar da faruwar wannan lamarin, wanda ya ce an kawo masu maganar a ranar 13 ga watan Satumbar 2025.
Ya ce, “Yarinyar ta samu ƙuna a marar ta, ɗuwawu da farji. Kwamishinan 'yan sanda, Sani Omolori Aliyu, ya bayar da umurnin a gaggauta kamo matar. Yanzu haka an tura maganar zuwa sashen binciken manyan laifuka don zurfafa bincike."
No comments