Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana cewa dakatarwar wucin-gadi da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi...
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana cewa dakatarwar wucin-gadi da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi na fitar da ɗanyar ƙwarar kaɗanya zuwa ƙasar waje wani muhimmin mataki ne da aka yi cikin hangen nesa domin zai buɗe sababbin damarmaki ga tattalin arzikin Nijeriya.
Ministan ya faɗi haka ne a matsayin sa na babban baƙo a Babban Taro na 20 na Yankin Arewa na Akantoci (ICAN) wanda aka yi a Minna, Jihar Neja.
Idris dai ɗan Jihar Neja ne, wadda ita ce cibiyar noman ƙwarar kaɗanya a Nijeriya.
A jawabin da ya gabatar ta bakin wakilin sa a taron, wato Darakta-Janar na Hukumar Muryar Nijeriya (VON), Malam Jibrin Baba Ndace, ministan ya ce: “Dakatarwar wucin-gadi kan fitar da ɗanyar ƙwarar kaɗanya da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi kwanan nan ba gwaji ba ne kawai, a'a mataki ne na hangen nesa don buɗe cikakkar damar haɓaka tattalin arzikin ƙasar nan.
"Ta hanyar kafewa kan cewa a riƙa sarrafa ƙwarar kaɗanya a cikin ƙasar nan, Shugaban Ƙasa yana tabbatar da cewa Nijeriya, wadda ke samar da sama da kashi 50 cikin ɗari na ƙwarar kaɗanya a duniya, ba za ta tsaya a matsayin mai sayar da ɗanyen kayayyaki kawai ba, sai dai ta zama jagora wajen samar da kayayyakin da aka yi da kaɗanya masu ƙima a duniya.”
Idris ya ce Jihar Neja, wadda cibiya ce ta noman ƙwarar kaɗanya, za ta amfana matuƙa da wannan tsarin.
A cewar sa, hakan zai jawo zuba jari, ya kawo fasaha ta zamani, ya bunƙasa ƙarfin sarrafa kayayyaki, kuma ya samar da ayyukan yi ga matasa da mata a karkara.
Ya ce: “Wannan babban matakin zai ƙarfafa zuba jari a cikin gida, ya kawo musanyar fasaha, ya kuma hanzarta bunƙasa ƙarfin sarrafa kayayyaki. Haka kuma zai samar da ingantattun ayyukan yi ga matasa da mata a ƙauyuka, ya haɓaka samun kuɗin musayar waje, tare da zurfafa matsayin Nijeriya a cikin harkokin cigaban ƙasa a duniya.”
Ministan ya yaba wa Ƙungiyar Masu Sana'ar Ƙwarar Kaɗanya ta Ƙasa (NASPAN) bisa goyon bayan da suka nuna, yana mai cewa Gwamnatin Tarayya tana samar da yanayi mai kyau don tabbatar da ganin cewa wannan hangen nesa na Shugaban Ƙasa ya tabbata.
Ya ƙara da cewa manufar gwamnati kan noman ƙwarar kaɗanya wani ginshiƙi ne a cikin gagarumin shirin Shugaban Ƙasa na farfaɗo da tattalin arziki, wanda ya ta’allaƙa kan fayyace gaskiya, da sake wayar da kan jama'a, da haɗa kowa da kowa a cikin tafiyar.
Ya kuma ambaci manyan ayyukan da gwamnati ke aiwatarwa, irin su gina Titin Bakin Teku na Legas zuwa Kalaba, da Babban Titin Sakkwato zuwa Badagiri, da gyaran layin dogo na yankin gabashin ƙasar nan.
Ya ce daga cikin kilomita 1,068 na titin ake ginawa daga Sakkwato zuwa Badagiri, kusan kilomita 125 za su ratsa ne ta cikin Jihar Neja.
Bugu da ƙari, ya bayyana yadda Gwamnatin Tarayya take amfani da tsarin TSA da na GIFMIS wajen rage ɓarna da tabbatar da ingantaccen sarrafa kuɗaɗen gwamnati.
Idris ya ce cigaban da Nijeriya ta samu a ma’aunin ƙungiyar Transparency International daga matsayi na 145 a 2023 zuwa 140 a 2024 ya samo asali ne daga aiwatar da muhimman matakai da aka yi, kamar cire tallafin man fetur da daidaita farashin musayar kuɗi.
Ya kuma yi kira ga ƙwararru a fannin lissafin kuɗi, wato akantoci, da sauran masana su haɗa kai da gwamnati wajen wayar da kan jama’a da kuma gina al’adar aiki da gaskiya da shugabanci nagari.
No comments