Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

DA ƊUMU-ƊUMI: Jerin Waɗanda Ba Za Su Biya Haraji Ba A Nijeriya. Ko Kana Ciki?

A wata hira da aka yi da Shugaban kwamitin gyaran haraji, Mr Taiwo Oyedele a tashar Channels ranar Talata, 8 ga watan Satumba, ya bayyana ce...


A wata hira da aka yi da Shugaban kwamitin gyaran haraji, Mr Taiwo Oyedele a tashar Channels ranar Talata, 8 ga watan Satumba, ya bayyana cewa sama da kashi 97 na 'yan Nijeriya ba za su biya haraji ba kwata-kwata. Mr Taiwo ya bayyana jerin Waɗanda biyan sabon harajin ba zai shafe su ba kamar haka:

1 Masu karban mafi ƙarancin Albashi na 70k zuwa ƙasa.

2 waɗanda kuɗin shigar su bai zarce dubu 100 ba a wata.

3 'Yan kasuwa masu jarin ƙasa da Naira Milyan 2

4 Kamfanoni da a da ake karban haraji a hannun su duk da kadarar su ba ta haura Naira Milyan 25 ba, yanzu sai kadarar su ta kai Naira Milyan 100 sannan za su biya haraji.

6 Waɗanda ke biyan tarin haraje-haraje ma ba a bar su a baya ba, domin daga sabuwar shekarar 2026 za su fara biyan haraji daya tal, kuma mafi ƙaranci.

Ko ta yaya mutum zai gane cewa bai cancanci biyan haraji ba?

Mr Oyedele ya ce tuni suka tanadi hatimi a manhajar QR kan shafin yanar gizo na tsarin harajin, inda duk mai buƙatar sanin matsayin sa zai je ya ɗauki hoton hatimin QR ɗin ya zura sunan sa da bayanin kuɗaɗen shigar sa don sanin ya dace ya biya haraji ko a'a.

No comments