Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa ta kashe sama da Naira Biliyan 2.08 domin tallafa wa ɗaliban manyan makarantu a shiyyar Arewa maso Yamma t...

Daraktan Hukumar Wayar da Kai ta Ƙasa (NOA) a Jihar Katsina, Alhaji Mukhtar Lawal-Tsagem ne ya bayyana hakan a Katsina, yayin wani taron wayar da kai da Ma’aikatar Ƙididdiga da Wayar da Kai ta shirya a ranar Talata.
Ya ce an raba kuɗin ga dalibai 20,919 daga jihohin Arewa maso Yamma domin biyan kuɗin makaranta da kuma tallafawa karatunsu.
Lawal-Tsagem ya kara da cewa, gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta bada tallafi ga Manoman alkama a kananan hukumomi 12 na Jihar Kebbi a karkashin shirin ta na NAGAP. A Jihar Kaduna kuma manoman citta sun samu tallafin Naira biliyan 1.6.
Ya ƙara da cewa, a Jihar Kebbi, an kaddamar da shirin samar da ruwa a Yawuri mai darajar Naira biliyan 2.
Shirin NELFUND na bayar da rancen bashi mara ruwa ga ɗaliban manyan makarantu, wanda zai taimaka musu wajen biyan kudin makaranta da sauran bukatun karatu.
No comments