Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Aikin Bututun Gas Na Ajakuta-kaduna-kano Na Cigaba Da Gudana Ba Ƙaƙƙautawa —Gwamnatin Tarayya

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa aikin bututun gas na Ajaokuta-Kaduna-Kano (AKK) na ci gaba da gudana cikin nasara, a wani yunƙuri na bunƙa...

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa aikin bututun gas na Ajaokuta-Kaduna-Kano (AKK) na ci gaba da gudana cikin nasara, a wani yunƙuri na bunƙasa masana’antu da habaka tattalin arzikin ƙasar.

Ministan Watsa Labarai da Wayar da Kai na ƙasa, Alhaji Mohammed Idris, ne ya bayyana hakan a birnin Minna, jihar Neja, a yayin taron Gwamnonin Jam’iyyar APC da Kwamishinonin Watsa Labarai daga jihohin da APC ke mulki suka halarta.

Mohammed Idris ya bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu na bai wa zuba jari a bangaren makamashi da ababen more rayuwa muhimmanci, domin ciyar da ƙasar gaba a matakin masana’antu. Ya ce aikin bututun AKK wanda ke da tsawon kilomita 614 daga Ajaokuta zuwa Kano, ta hanyar Abuja da Kaduna, ya riga ya ƙetare Kogin Neja, kuma yana tafiya tare da aikin bututun Obiafu–Obrikom–Oben (OB3), duka a wani bangare na shirin Bututun Iskar Gas da kewaye Nijeriya na (Trans-Nigeria Pipeline Project)

Ministan ya ƙara da cewa, gwamnatin Tinubu ta ƙaddamar da wasu muhimman ayyuka kamar Masana’antar samar da Gas ta ANOH da AHL, waɗanda za su samar da Gas da ya kai kimanin Cubic Feet miliyan 500 a kullum, ƙarin kashi 25 cikin 100 na gas ɗin da ake samarwa a cikin gida.

Haka kuma, ya ce an soma gina wasu ƙananan masana’antun sarrafa gas guda biyar a Ajaokuta, tare da janyo hannun jari na sama da dala miliyan 500 a bangaren CNG, domin samar da makamashi mai arha ga gidaje da masana’antu.
 

Minista Idris ya kuma bayyana cewa Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta bada tallafi da lamunin inganta sana’o’i ga sama da ‘yan Nijeriya 900,000 ta hanyar shirin ‘Presidential Conditional Grant and Loan Scheme’, domin tallafa wa ‘yan kasuwa ƙanana, masu sana’o’i, da matasan ‘yan kasuwa a fadin ƙasar.

Ya ce sama da ɗalibai 300,000 suna amfana da sabon tsarin lamunin karatu, wanda ke tabbatar da cewa babu wani matashi da zai rasa damar zuwa jami’a saboda rashin kuɗin makaranta.

Ya ci gaba da cewa, Gwamnatin Tarayya ta kuma sanya hannu kan shirin bunƙasa noma da masana’antun sarrafa amfanin gona, ta hanyar ƙara wa Bankin Noma ƙarfi da Naira tiriliyan 1.5 domin bai wa manoma da ‘yan kasuwa a bangaren noma jari.

Ya ce a bangaren bunƙasa matasa da basira, gwamnatin ta ware Naira biliyan 75 don tallafa wa kananan masana’antu da masu sana’a, sannan ta ware Naira biliyan 120 da aka tanada domin horar da masu sana’ar hannu da fasaha, da nufin tallafa wa matasa miliyan 10 a fadin kasa.

Har ila yau, shirin Three Million Technical Talent (3MTT) na bai wa matasa damar koyon fasahar zamani, inda aka kaddamar da cibiyar 3MTT a Kano kwanan nan.

"A bangaren ƙirƙire-ƙirƙire da tattalin arzikin, gwamnati ta samar da Creative Economy Development Fund (CEDF) wanda ke bayar da tallafi har zuwa $100,000 ga masu kasuwanci, tare da ƙarin tallafi daga Naira 500,000 zuwa Naira miliyan 2 ga matasa ta hanyar Nigeria Youth Investment Fund," in ji Ministan.
 

No comments