Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Soja Ya Lakaɗa Wa Mai Gyaran Waya Duka Har Lahira Saboda Jinkiri Wajen Gyaran Wayar Budurwarsa

Wani sojan Nijeriya mai muƙamin Lance Kofur mai suna Ahmada A ya lakaɗa wa wani mai gyaran waya Alkasum Ibrahim duka har lahira. Lamarin ya ...


Wani sojan Nijeriya mai muƙamin Lance Kofur mai suna Ahmada A ya lakaɗa wa wani mai gyaran waya Alkasum Ibrahim duka har lahira.

Lamarin ya faru ne a unguwar Mayo-Belwa da ke jihar Adamawa, sakamakon jinkirin gyaran wayar budurwar tasa.

Sahara Reporters ta ruwaito cewa sojan da ake zargin ya kai wa mai gyaran waya, Alkasum Ibrahim hari ne a ranar Larabar da ta gabata bayan budurwar tasa ta yi ƙorafin cewa ba a gyara wayarta a kan lokaci ba.

Shaidu sun ce budurwar ta ɗauki wayarta zuwa shagon Alkasum tun da farko, amma gyaran ya samu jinkiri saboda wasu dalilai da ba a bayyana ba. Jin jinkirin da aka samu ya vata mata rai, inda aka ce ta tuntubi saurayinta.

Jim kaɗan sai sojan ya kutsa cikin shagon tare da yi wa matashin duka kawo wuƙa.

An bar Alkasum a sume kuma daga baya ya mutu sakamakon raunukan da ya samu.

Lamarin dai ya tayar da hankalin jama’a, inda da dama ke yin kira da a yi adalci tare da yin Allah wadai da yadda jami’an soji ke amfani da ƙarfi kan fararen hula.

No comments