Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya dage ziyarar da ya shirya kaiwa garin Iperu da ke Jihar Ogun a gobe Alhamis, inda aka tsara zai kaddamar da fa...
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya dage ziyarar da ya shirya kaiwa garin Iperu da ke Jihar Ogun a gobe Alhamis, inda aka tsara zai kaddamar da fara ayyuka a Filin Jirgin Sama na Kayayyaki na Gateway International.
Maimakon haka, Shugaban zai nufi birnin Jos, babban birnin Jihar Filato, domin jajantawa gwamnati da al’ummar jihar kan hare-haren bindiga da aka kai kwanan nan, wadanda suka yi sanadin rayukan mutane da ba su ji ba ba su gani ba.
Daga Jihar Filato bayan Jajantawa mutanen da harin bindiga ya shafa, Shugaba Tinubu Zai nufi Legas domin gudanar da bukukuwan ranar Good Friday.
A ranar Asabar, 4 ga Afrilu zai je Jihar Ogun domin Kaddamar da Filin Jirgin Sama na Kayayyaki da kuma jiragen sama guda biyu na kasuwanci don fitar da kaya da shigo da su, domin bunkasa tattalin arzikin jihar.
Haka nan, zai kaddamar da sabon ginin sashin gudanarwa na Hukumar Kwastam (FOU) da motocin aikinsu.
Shugaban Zai koma Legas daga nan don ci gaba da hutun Ista, inda zai kaddamar da manyan ayyuka da gwamnatin Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya samar. Ayyukan sun hada da:
Gadar mahada ta Ojota zuwa Opebi.
Ginin bayanan kasa na Jihar Legas (GIS Building).
Katafaren ginin hukumomi da aka sanyawa sunan Shugaban Kasa.
Sabon rukunin makarantu.
Sannan Kafin ya koma Abuja, Shugaba Tinubu zai ziyarci Jihar Bayelsa a ranar 10 ga Afrilu, domin kaddamar da wasu ayyukan da Gwamna Duoye Diri ya kammala.

No comments