Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

HUKUNCIN KISA: Sheikh Abduljabbar Ya Kai Koke Ga Alƙalin Alƙalai Kan Ɗaukaka Ƙara

Fitaccen Malamin addini a Kano, Sheikh Abduljabbar Nasir Kabara, ya miƙa ƙorafi ga Alƙalin Alƙali na Ƙasa (CJN), yana zargin cewa ana jinkir...

Fitaccen Malamin addini a Kano, Sheikh Abduljabbar Nasir Kabara, ya miƙa ƙorafi ga Alƙalin Alƙali na Ƙasa (CJN), yana zargin cewa ana jinkirta shari’ar ɗaukaka ƙarar da ya shigar ga gangan tare da wasu kura-kurai a tsarin gudanar da shari’ar.

Ƙorafin, wanda aka shigar ƙarƙashin lambobin shari’a CA/KN/01/2025 da K/93CA/2022, ya buƙaci Alƙalin Alƙalai na Ƙasa da ya tabbatar da cewa an gudanar da shari’ar cikin adalci da kuma gaggawa.

A cikin wasiƙarsa, Sheikh Kabara ya nuna damuwa kan wasu tangarɗa na gudanarwa da yake zargin suna kawo tsaiko ga shari’ar, da kuma wahalar samun cikakkun bayanan rubutattun hujjojin da aka gabatar a Babbar Kotun Jihar Kano. Haka kuma, ya bayyana cewa yanayin siyasa da zamantakewa da ke tattare da shari’ar na iya shafar adalcin da ya kamata a samu a ɓangaren shari’a.

A watan Disambar 2022 ne Kotun Shari’ar Musulunci ta Ƙoli a Kano, ƙarƙashin jagorancin Alƙali Mallam Ibrahim Sarki Yola, ta yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya, bayan samunsa da laifin furta kalaman da ake ganin sun saɓa wa Annabi Muhammad (SAW) yayin wa’azinsa. 

Bayan wannan hukunci, ya ɗaukaka ƙara yana ƙalubalantar sahihancin hukuncin, inda ya jingina hujjojinsa kan rashin ba shi cikakken damar kare kansa, tambayoyi kan ikon kotun da ta yanke hukuncin, da kuma cewa kalaman da ya furta sun fito ne daga binciken ilimi, ba da niyyar yin saɓo ba.

A cikin ƙorafin da ya gabatar, Sheikh Kabara ya buƙaci Babban Alƙalin Ƙasa ya yi amfani da ikon sa na kula da tsarin shari’a domin tabbatar da cewa Kotun Ɗaukaka Ƙara ta Kano, ko wata rassa ta daban, ta saurari shari’ar ba tare da wani katsalandan ba. Ya jaddada cewa bai aikata laifin da ake tuhumarsa da shi ba, yana mai cewa gaskiya za ta bayyana idan aka gudanar da shari’a cikin gaskiya da buɗaɗɗen tsari.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, Ofishin Babban Alƙalin Ƙasa bai fitar da wata sanarwa kan wannan ƙorafi ba, yayin da gwamnatin Jihar Kano ke ci gaba da tsayawa kan sahihancin hukuncin da aka yanke a farko. 

No comments