Daga Ibrahim Muhammad, Kano Ƙungiyar Kwankwasiyya ta sanar da cewa Mataimakin Gwamnan Jihar Kano ya miƙa takardar yin murabus daga muƙamin ...
Ƙungiyar Kwankwasiyya ta sanar da cewa Mataimakin Gwamnan Jihar Kano ya miƙa takardar yin murabus daga muƙamin sa.
Wannan na cikin sanarwar da mai magana da yawun ƙungiyar, Dakta Habibu Sale Mohammed ya fitar a ranar Juma'a 27 ga watan Maris, 2026.
Sanarwar ta bayyana cewa an ɗauki wannan matakin ne domin tabbatar da zaman lafiya da kuma bai wa ofishin damar gudanar da aikin sa yadda ya kamata ba tare da tangarɗa ba.
Sanarwar ta kuma ce murabus ɗin ba yana nufin amincewa da zarge-zargen da Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi ba.
Mataimakin Gwamnan ya kuma jaddada cewa yana da tsaftataccen tarihi a aikin gwamnati.
Sanarwar ta ƙara da cewa ya ɗauki matakin ne domin kauce wa rikice-rikicen siyasa da ka iya kawo tsaiko ga tafiyar gwamnati da ci gaban jihar.
Haka kuma sanarwar ta bayyana cewa Gwarzo, zai mayar da hankali wajen ƙarfafa ƙungiyar Kwankwasiyya da tsara dabarun siyasa gabanin zaɓen 2027.
Ƙungiyar ta kuma buƙaci magoya bayan ta da al’ummar jihar da su kasance masu bin doka tare da ci gaba da goyon bayan shugabanci nagari.
Sai dai har ya zuwa haɗa wannan rahoto, ba mu samu jin ta bakin mataimakin Gwamnan ba, ba mu kuma ga wata sanarwa da ya fitar ko aka fitar da yawun sa gake da wannan mataki ba.

No comments