Daga Ibrahim Muhammad, Kano Jam'iyyar NDC ta zabi fitacce ɗan siyasa a jihar Kano, Hon.Husaini Isah Mairiga a matsayin sabon shugaban ja...
Daga Ibrahim Muhammad, Kano
Jam'iyyar NDC ta zabi fitacce ɗan siyasa a jihar Kano, Hon.Husaini Isah Mairiga a matsayin sabon shugaban jam'iyyar na Kano.
Zaben na Hon. Husaini Isa Mairiga ya biyo bayan taron da masu ruwa da tsaki na jam'iyyar suka gudanar ne a Abuja ranar Alhamis. Meriga ya taba riƙe sakataren jam'iyyar SDP na jihar Kano.
Sabon shugaban jam'iyyar, a lokacin mulkin Shekarau ya riƙe muƙaminmai bai wa Gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau shawara akan harkokin siyasa.
A jawabin sa bayan tabbatar da shi a matsayin shugaban jam'iyyar NDC na jihar Kano, Hon. Husaini Isa Mairiga ya yi wa Allah godiya, inda ya ce ba dabara ko wayon sa ne ta sa suka sami wannan matsayi ba. Don haka suna roƙon Allah ya sa jam'iyyar ta karbu a Kano da ƙasa baki ɗaya.
Daga nan ya yi nuni da cewa dama ita jam'iyyar NDC, ba sabuwa ba ce, an dai yi mata gyara ne domin daɗa ingantata. Don haka suna roƙon al'ummar jihar Kano, musamman matasa da manya maza da mata su yi ƙoƙari wajen shiga jam'iyyar, musamman idan aka yi la'akari da yadda sauran jam'iyyu suka zama na son zuciya da yin kama karya da abubuwa da yawa marasa daɗi.
Hon. Husaini Isa Mairiga ya ce jam'iyyar NDC ta al'umma ce, kuma za su yi ƙoƙari na ganin ci gaban jam'iyyar, kuma za su fitar da sunayen shugabannin ta na jihar Kano a hukunance, tare da tabbatar da su ga hukumar zabe ta ƙasa da ta jihar Kano da hukumomin tsaro.

No comments