Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Farfesa Bugaje Zai Ci Gaba Da Shugabantar Hukumar NBTE A Karo Na Biyu, Na Shekaru Biyar

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da sabunta naɗin Farfesa Idris Muhammad Bugaje a matsayin Sakataren Gudanarwa na Hukumar Kula da I...



Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da sabunta naɗin Farfesa Idris Muhammad Bugaje a matsayin Sakataren Gudanarwa na Hukumar Kula da Ilimin Fasaha ta Kasa (NBTE) karo na biyu kuma na ƙarshe, na tsawon shekara biyar.

Farfesa Bugaje, wanda aka fara naɗawa wannan muƙami a ranar 14 ga watan Maris na shekarar 2021 don wa’adin farko, zai ci gaba da jan ragamar hukumar sakamakon abin da fadar shugaban ƙasa ta kira "ƙoƙari da nuna ƙwarewa" wajen gudanar da aiki.

Sanarwar da Mai Magana da Yawun Shugaban Ƙasa kan Harkokin Yaɗa Labarai da Dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Laraba, 1 ga watan Afrilu, 2026, ta bayyana cewa Shugaba Tinubu ya ɗauki wannan mataki ne bayan gudanar da bincike mai zurfi kan ayyukan Farfesan.

Fadar shugaban ƙasar ta yaba da yadda aka samu gagarumin sauyi a fannin ilimin sana’o’i da fasaha (TVET) ƙarƙashin jagorancin sa, wanda hakan ke tafiya daidai da manufar 'Kyakkyawan Fata' (Renewed Hope) na gwamnatin Tinubu.

Cikin nasarorin da aka lissafa cewa Farfesa Bugaje ya samar a wa’adin sa na farko sun haɗa da:
 * Fasalta tsarin ilimin fasaha na Nijeriya domin ya dace da zamani.
 * Sabunta manhajojin karatu da samar da sababbi guda 100 don dacewa da buƙatun kasuwar ƙwadago ta duniya.
 * Ƙarfafa gwiwar matasa wajen rungumar dogaro da kai ta hanyar ƙwarewa.

Daga ƙarshe, Shugaba Tinubu ya buƙaci Sakataren na NBTE da ya yi amfani da wannan damar ta wa’adi na biyu wajen ɗorewa da kyawawan manufofin da ya fara, tare da kammala muhimman ayyukan da ke gaban hukumar domin ciyar da ƙasar gaba.

No comments