Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya kafa Kwamitin Kamfanonin Fasahar Hadahadar Biyan Kuɗi na Zamani (PSPC), wato 'Payment Service Providers...
Gwamnan CBN, Olayemi Cardoso, ne ya ƙaddamar da kwamitin a taron farko da aka yi a Lagos a makon nan.
Daga cikin manyan ayyukan kwamitin shi ne tsara sabuwar manufa ta tsarin biyan kuɗi. Haka kuma kwamitin ya haɗa da CBN, da Hukumar Sadarwa ta Nijeriya (NCC), Hukumar Kariya ga Masu Ajiya (NDIC), da Hukumar Kula da Kasuwar Hannayen Jari (SEC), da kuma 'Nigeria Inter-Bank Settlement System Plc' (NIBSS).
Wannan ya nuna fara wani tsari mai ƙarfi na haɗin gwiwar hukumomi kan batutuwan da suka shafi tsarin biyan kuɗi a Nijeriya.
Mataimakin Gwamnan CBN mai kula da bangaren Manufofin Tattalin Arziki, Muhammad Sani Abdullahi, ya bayyana cewa an kafa kwamitin ne domin ƙarfafa daidaiton manufofi, zurfafa musayar ilimi, da kuma sauƙaƙa warware matsaloli tare a wani fanni da ke ƙara zama ginshiƙi ga bunƙasar tattalin arziki.
Ya ce CBN na shirin ƙaddamar da sabuwar manufa ta tsarin biyan kuɗi, wadda za ta tsara makomar tsarin kuɗaɗen dijital na Nijeriya cikin shekaru uku masu zuwa.
Abdullahi ya ce: “A cikin ’yan shekarun nan, tsarin biyan kuɗi ta hanyar dijital a Nijeriya ya samu gagarumin ci gaba.
A shekarar 2024 kaɗai, an gudanar da sama da biliyan 11.2 na ma’amaloli ta hanyoyin zamani, wanda adadin kuɗin ya kai sama da naira tiriliyan dubu, wato 'quadrillion' 1.07 kenan.
Wannan shi ne karo na farko da biyan kuɗi ta dijital ya wuce wannan mataki, wanda ke nuna babban ci gaba.
“Wannan ci gaba ya ƙara habaka ne a 2025, haka kuma a watannin farko na 2026. Wannan fanni yana bunƙasa sosai, kuma yana da tasiri mai girma ga tattalin arzikin Nijeriya da haɓakar da ya haɗa kowa da kowa da kasuwanci da sauran alfanun ƙasa.
“Saboda haka ya zama dole CBN ya ƙaddamar da wannan kwamiti domin ƙarfafa haɗin kai a manufofi, musayar ilimi, da kuma tabbatar da warware matsaloli tare tsakanin masana’antu da Babban Banki.”
Ya ƙara da cewa kafin kafa kwamitin, hulɗa tsakanin masu gudanar da harkokin hadahadar kudade da masu tsara dokoki tana yawan zama rarrabe, kuma hakan kan jinkirta magance matsaloli. Sabon tsarin, a cewar sa, zai taimaka wajen saurin warware matsaloli da kuma samar da manufofi cikin sauri.
Dangane da sabuwar manufa, ya ce: “Cikin kusan wata guda daga yanzu, za mu ƙaddamar da sabuwar manufa ta tsarin biyan kuɗi wadda za ta fayyace inda muke son tsarin ya dosa cikin shekaru uku masu zuwa. An tsara wannan manufa tare da haɗin gwiwar kamfanonin fasahar kuɗi, masu gudanar da kuɗin wayar hannu, da masu ba da sabis na biyan kuɗi.”
Mataimakin Gwamna mai kula da Tsaron Tsarin Kuɗi, Philip Ikeazor, ya ce za a aiwatar da sabbin manufofi na kai-tsaye don yaƙi da halasta kuɗin haram da kuma damfara a bankuna da masu ba da sabis na biyan kuɗi domin ƙarfafa tsaro.
Ya ce: “Dangane da rage haɗarin damfara, mun ga cewa yawan damfara ya ragu da kashi 50 tsakanin 2024 da 2025. Mun kuma fito da sabuwar manufa ta atomatik don yaƙi da halasta kuɗin haram da damfara, wadda za ta taimaka matuƙa wajen rage irin waɗannan laifuka idan aka aiwatar da ita a bankuna da masu ba da sabis na biyan kuɗi.”
Har ila yau, Manajan Darakta na NIBSS, Premier Oiwoh, ya yaba wa CBN bisa wannan mataki, yana mai cewa hakan zai ƙara bunƙasa tsarin biyan kuɗi a ƙasar.
Daga ɓangaren masana’antu kuma, Shugabar EFInA, Foyinsolami Akinjayeju, ta ce: “Mun samu gagarumin ci gaba a haɗa jama’a cikin harkar kuɗi sakamakon kirkire-kirkire daga masu ba da sabis na kuɗi da ba bankuna ba, musamman a fannin biyan kuɗi. Don haka rawar da masu ba da sabis na biyan kuɗi za su taka wajen ƙarfafa ci gaban da ya haɗa kowa na da matuƙar muhimmanci. Wannan dandali mataki ne mai kyau domin samar da mafita cikin gaggawa ga matsalolin da ke damun tsarin biyan kuɗi a Najeriya.”

No comments