Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Yadda Aka Gudanar Da Taron Yi Wa Shugaba Tinubu Addu'ar Samun Nasarar Mulki

A kwanakin baya ne aka gudanar da wani taro na musamman a ɗakin taro na Arewa House da ke Kaduna domin yi wa Shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu...

A kwanakin baya ne aka gudanar da wani taro na musamman a ɗakin taro na Arewa House da ke Kaduna domin yi wa Shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu addu'ar samun nasara a shugabancin da ya ke yi wa al'ummar Nijeriya.

Ƙungiyar 'Arewa Think Tank', wacce Muhammad Alhaji Yakubu ke jagoranta ne ta gudanar dabl taron, inda aka gayyato Alarammomi suka sauke Alƙur'ani mai girma, tare da yin addu'o'i ga shugaba Tinubu.

Shugaban shirya wannan taro, Muhammad Alhaji Yakubu ya bayyana cewa sun shirya taron ne domin nema wa Nijeriya ci gaba, ta hanyar yi wa jagoran Nijeriyar addu'o'i na musamman don neman Allah ya shige masa gaba, ya ba shi damar aiwatar da ayyukan da za su ciyar da ƙasa gaba ta kowanne fanni.

Ya ce duk da cewa shugaba Tinubu na yin bakin ƙoƙarin sa, amma dai yana neman addu'o'in al'umma domin Allah ya yi masa jagora.

A nasa jawabin, Marafan Zuru, Dokta Sule Iko Sani Sami ya bayyana cewa shugabanni masu riƙe da madafun iko da cewa mutane ne da ke buƙatar a yi masu addu’a ta ƙwarai domin samun nasarar gudanar da jagoranci su.

Marafan na Zuru ya ce hakan ne ta sa aka yi wannan gagarumin taro domin yi wa shugaba Bola Ahmed Tinubu addu’a ƙarƙashin jagorancin ƙungiyar 'Arewa Think Tank.' 

Shi kuwa a nasa jawabin, Sanata Tijjani Yahaya Ƙaura, Tsohon Ministan ma'aikatar kula da harkokin ƙasashen wajen Nijeriya, ya bayyana cewa a matsayin sa na cikakken ɗan ƙasa Nagari ya na da gagarumar dama da ikon zuwa ya haɗu da sauran 'yan Nijeriya domin yi wa shugaba Bola Ahmed Tinubu addu'ar samun nasara a kowane fanni domin yi wa shugaba addu'a yi wa ƙasa addu'a.

Ya ce, "Don haka yi wa shugaba Bola Ahmed Tinubu addu'a, mutum na yin addu'a ne kai tsaye domin samun ingantaccen tsaro ga ƙasa da al'ummar ta baki ɗaya. Saboda haka ne na zo nan inda aka taru aka yi wa shugaban ƙasa addu'a."

Tijjani Ƙaura ya ce ya zo ne domin ya wakilci Sanata Abdul'aziz Abubakar Yari, wanda ya kasance a kan gaba-gaba wajen goyon bayan shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Tun da farko da yake gabatar da jawabin sa tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Alhaji Muktar Ramalan Yero, kira ya yi ga jama'a da su riƙa gaya wa shugabanni gaskiya akodayaushe, domin ta haka ne za a samu al'amuran ƙasa su inganta.

Ya kuma yi kiran faɗakarwa ga jama'a da su riƙe gaskiya da amana, abin da ya bayyana da cewa babbar hanya ce ta samu ci gaban da kowa ke bukata.

Muktar Yero, ya bayyana taron 'Arewa Think Tank da cewa shi ne karo na Uku da suka yi duk da nufin ci gaban ƙasa.



No comments