Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Cikar FRCN Shekara 75: Tinubu Yana Zamanantar Da Kafafen Yaɗa Labarai – Minista

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya ce Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu yana ci gaba da jajircewa wajen zamanant...

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya ce Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu yana ci gaba da jajircewa wajen zamanantar da kafafen yaɗa labarai na gwamnati da tabbatar da cewa kowane ɗan Nijeriya na samun labarai.

Idris ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a Abuja a lokacin ƙaddamar da tambarin cikar shekara 75 na Hukumar Rediyon Tarayyar Nijeriya (FRCN), wanda ya buɗe jerin shirye-shiryen bikin cikar shekarun.

Ya ce gwamnatin tana zuba jari a fannin watsa shirye-shirye domin ƙarfafa kafafen yaɗa labarai.

Ya ƙara da cewa ana girka sababbin na’urorin tiransimita na rediyo masu ƙarfin kilowatt 50 a Kaduna, Ibadan, Inugu da Gwagwalada.

Ya ce: “Da waɗannan sababbin na’urorin, FRCN za ta ƙara faɗaɗa tasirin ta a fagen aikin rediyo a Nijeriya. Wannan yana nuna ƙudirin wannan gwamnati na zamanantar da kafafen yaɗa labarai.”

Ministan ya jaddada cewa gyare-gyaren da ake yi a ɓangaren yaɗa labarai ba su tsaya kan ababen more rayuwa kaɗai ba, har ma sun haɗa da tsare gaskiya a aiki, ɗaukar nauyi da kuma haɗa jama’a a harkokin mulki.

Ya ce: “Kafafen yaɗa labarai masu ƙarfi da kuma jama’a masu shiga harkokin ƙasa su ne ginshiƙai biyu na dimokiraɗiyya mai inganci,” yana mai kira ga FRCN da ta ci gaba da haskaka muradun ’yan Nijeriya tare da ƙarfafa tattaunawa mai amfani ga ƙasa.

Idris ya bayyana FRCN a matsayin muhimmiyar hukuma ta ƙasa wadda ta taka rawa wajen haɗa kan ’yan Nijeriya tsawon shekaru 75.

Ya ƙara da cewa: “Tsawon wannan lokaci, FRCN ba ta tsaya kan watsa shirye-shirye kaɗai ba, har ma ta taimaka wajen bunƙasa rayuwar jama’a da kuma haɗa kan ƙasa.”

Ministan ya yaba wa shugabanci da ma’aikatan hukumar bisa jajircewar su, yana mai cewa tambarin da aka ƙaddamar alama ce ta amincewa da kuma alƙawari ga makoma mai kyau.

A nasa jawabin, Darakta-Janar na FRCN, Dakta Mohammed Bulama, ya gode wa Gwamnatin Tarayya bisa goyon bayan da take bai wa hukumar, yana mai cewa bikin cika shekara 75 na hukumar yana nuna tunawa da tarihin FRCN da kuma sabuwar jajircewa ga ƙirƙire-ƙirƙire, ƙwarewa, da watsa labarai na jama’a.

Ya kuma tabbatar da cewa hukumar za ta ci gaba da daidaita kan ta da sababbin fasahohi tare da ci gaba da aiwatar da aikin ta na sanarwa, ilimantarwa da haɗa kan ’yan Nijeriya.

A cikin waɗanda suka halarci taron akwai Mashawarci na Musamman ga Shugaban Ƙasa kan Harkokin Kafofin Watsa Labarai da Sadarwa, Cif Sunday Dare; Babban Sakataren Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Ogbodo Chinasa Nnam; tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Jakada Babagana Kingibe; Darakta Janar na gidan rediyon Muryar Nijeriya (VON), Malam Jibrin Baba Ndace; Darakta-Janar na Hukumar Talbijin ta Nijeriya (NTA), Malam Salihu Abdulhamid Dembos; Sakataren Zartarwa na Ƙungiyoyin Watsa Labarai na Nijeriya (BON); Darakta-Janar na Hukumar Kula da Watsa Labarai ta Ƙasa (NBC), Dakta Charles Ebuebu; Dakta Yemisi Bamgbose; Shugaban Ƙungiyar ‘Yan Jarida ta Nijeriya (NUJ), Alhassan Yahya Abdul; Shugaban Ƙungiyar Ma’aikatan Rediyo, Talbijin, Finafinai da Harkokin Fasaha (RATTAWU), Yarima Emeka Kalu, da sauran manyan baƙi.




 

No comments