Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Jami’ar ABU Zariya Ta Karɓi Naira Biliyan 1.3 Daga NELFUND Domin Tallafa Wa Ɗalibai Sama Da 17,000

Jami’ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zariya a jihar Kaduna ta tabbatar da karɓar sama da naira biliyan 1.3 daga Asusun Bada Lamunin Karatu (NELF...


Jami’ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zariya a jihar Kaduna ta tabbatar da karɓar sama da naira biliyan 1.3 daga Asusun Bada Lamunin Karatu (NELFUND) domin tallafa wa ɗalibanta a shekarar 2026.

A wata takarda mai ɗauke da kwanan wata 17 ga Maris, 2026, ofishin mataimakin shugaban jami’ar ya bayyana cewa kuɗin sun kai naira biliyan 1,301,584,250, wanda aka tura cikin asusun jami’ar a matsayin lamunin ilimi ga ɗalibai.

Takardar ta ƙara da cewa kuɗin sun amfanar da ɗalibai 17,599, inda aka raba su kashi uku kamar haka:
•    Kashi na farko: ɗalibai 7,570 sun karɓi naira Miliyan 545,144,750
•    Kashi na biyu: ɗalibai 7,572 sun karɓi naira Miliyan 571,204,125
•    Kashi na uku: ɗalibai 2,457 sun karɓi naira Miliyan 185,235,375

Hukumar jami’ar ta nuna jin daɗinta ga wannan tallafi, tana mai cewa hakan zai taimaka matuƙa wajen sauƙaƙa wa ɗalibai nauyin karatu da kuma inganta harkokin ilimi.

A ƙarshen saƙon, jami’ar ta gode wa NELFUND bisa rawar da take takawa wajen tallafa wa ɗalibai, tare da jaddada muhimmancin irin wannan shiri wajen bunƙasa ilimi a ƙasar.
 

No comments