Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana ƙwarin gwiwar cewa shirye-shiryen garambawul da gwamnatin sa ke yi sun fara samar da sakamako mai kyau,...
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana ƙwarin gwiwar cewa shirye-shiryen garambawul da gwamnatin sa ke yi sun fara samar da sakamako mai kyau, duk kuwa da matsalolin tattalin arziki da ake fuskanta.
A wani saƙo na musamman da ya fitar ranar Lahadi domin murnar zagayowar ranar haihuwar sa karo na 74, shugaban ya gode wa ‘yan Nijeriya kan irin addu’o’i da nuna ƙauna da suka yi masa.
Kamar yadda ya saba a kowace shekara, Shugaba Tinubu ya bayyana cewa ya zabi gudanar da bikin murnar ranar haihuwar tasa ne cikin natsuwa, ba tare da wata hayaniya ba, bisa la'akari da yanayin da ƙasa ke ciki.
Ya kuma miƙa godiyar ga matar sa, Uwargida Oluremi Tinubu, da kuma Mataimakin sa Kashim Shettima kan kalaman yabo da suka yi gare shi.
Shugaban ya yarda cewa matakan gyara da gwamnatin sa ta ɗauka sun zo da ƙalubale, amma ya bayyana cewa an fara samun sauƙ.
> "Ina farin cikin cewa sadaukarwar da muka yi ba ta tafi a banza ba, domin muna iya hango haske a ƙarshen ramin wahala, duk da tasgaron da rikicin Gabas Ta Tsakiya ya haifar," in ji shugaban.
Shugaba Tinubu ya ƙara da cewa nasarorin da aka samu ba na shi kadai ba ne, a’a, na ɗaukacin ‘yan Nijeriya ne da suka nuna juriya da kishin ƙasa.
Yayin da gwamnatin ke dab da cika shekara uku da rantsarwa, shugaban ya tabbatar wa ‘yan ƙasa cewa yana da yakinin za a gina Nijeriya mai albarka ga na yanzu da kuma na gobe.
Daga ƙarshe ya buƙaci 'yan Nijeriya da su ci gaba da ba shi haɗin kai domin gina ƙasa mai ƙarfi wacce za ta zama abin alfahari ga nahiyar Afirka baki ɗaya.

No comments