Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Maniyyatan Maƙarfi Su 96 Sun Samu Gudumawar Harami Daga Alhaji Mai Ƙwai

Wani sanannen ɗan kasuwa, kuma mai taimakon jama'a, Alhaji Garba Mai Ƙwai ya agaza wa Maniyyatan aikin Hajjin bana su 96 daga Ƙaramar Hu...


Wani sanannen ɗan kasuwa, kuma mai taimakon jama'a, Alhaji Garba Mai Ƙwai ya agaza wa Maniyyatan aikin Hajjin bana su 96 daga Ƙaramar Hukumar Maƙarfi ta jihar Kaduna, inda ya tallafa wa Kowanne daga cikin su da yadukan Harami.

Maniyyatan daga Ƙaramar Hukumar ta Maƙarfi, waɗanda suka ƙunshi mata 29 da maza 67, sun karbi wannan Harami ne a lokacin da ake gudanar da bita da sauran koyarwa don aikin Hajjin, wanda ke gudana a sakatariyar Ƙaramar Hukumar da ke Maƙarfi a ranakun Asabar da Lahadi.

Cikin jawabin sa wajen miƙa wannan Harami, Alhaji Garba Mai Ƙwai ya yi fatan maniyyatan za su yi aikin Hajji karbabbe, tare da yin kira gare su su mayar da hankali wajen ibada da yi wa ƙasa addu'ar samun zaman lafiya da ci gaba mai ɗorewa.

Hukumar kula da jin daɗin Alhazai ta jihar Kaduna ta tabbatar da cewa dukkan maniyyatan 96 sun samu Bizar su ta tafiya aikin ibadar.





 

No comments