Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Ministan Yaɗa Labarai Ya Taya Tinubu Murnar Cika Shekara 74

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya taya Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu murnar cika shekara 74, yana mai bayya...

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya taya Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu murnar cika shekara 74, yana mai bayyana shi a matsayin jagora wanda salon jagorancin sa da gyare-gyaren sa suke ci gaba da tasiri wajen bunƙasa Nijeriya.

A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, Idris ya ce wannan lokaci ne na tuna irin gudunmawar da Shugaban Ƙasar yake bayarwa wajen cigaban ƙasa da kuma jajircewar sa wajen kawo sauye-sauye masu ma’ana.

Ya ce: “Wannan lokaci ne na murnar jagora wanda jarumtaka da hangen nesan sa suke ci gaba da jagorantar Nijeriya a wannan lokaci na gyare-gyare da farfaɗowar ƙasa.”

Ministan ya ƙara da cewa shirin Shugaban Ƙasa Tinubu na ɗaukar matakai masu wahala sun sanya ƙasar nan kan turbar bunƙasa da daidaito na dogon lokaci.

Ya kuma bayyana cewa mayar da hankali kan tsare gaskiya, sadarwar da ta dace da haɗin kan ƙasa na ci gaba da jagorantar ayyukan ma’aikatar.

Ya ce ƙarfafa sadarwa mai tsari da hulɗa da jama’a da kuma yaƙi da yaɗa bayanan ƙarya suna nuna muhimmancin gaskiya da amincewa a harkokin mulki.

Idris ya faɗa wa Shugaban Ƙasa: “A yayin da kake bikin wannan rana ta musamman, muna yaba maka bisa hidimar ka ga ƙasa da kuma jajircewar ka wajen gina Nijeriya mai amfani ga kowa." 

Ya kuma yi addu’ar Allah ya ƙara masa lafiya, ƙarfi da hikima wajen ci gaba da jagorantar ƙasar nan zuwa ga cigaba mai ɗorewa.
 

No comments