Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya sanar da kafa wani sabon asusu na musamman domin tallafawa sojojin Nijeriya, musamman waɗanda suka jikk...
Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya sanar da kafa wani sabon asusu na musamman domin tallafawa sojojin Nijeriya, musamman waɗanda suka jikkata a bakin aiki da kuma iyalan waɗanda suka rasu yayin hidimar ƙasa.
Shugaban ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi, yayin da yake bikin cika shekaru 74 da haihuwarsa, inda ya ce wannan mataki na nufin girmama jaruntaka da sadaukarwar dakarun ƙasar.
A cewarsa, ya umarci Akanta Janar na Tarayya da ya buɗe wani asusu na musamman domin gudanar da wannan shiri, wanda zai mayar da hankali kan tallafa wa waɗanda suka ji rauni a fagen fama, da kuma zawarawa, mazaje, da ‘ya’yan waɗanda suka rasa rayukansu suna kare ƙasa.
A matsayin gudummawarsa ta kai tsaye, Shugaban ya yi alƙawarin bayar da dukkan albashinsa tun daga lokacin da ya hau mulki a matsayin tallafi na farko domin fara gudanar da asusun.
Shugaba Tinubu ya kuma yi kira ga gwamnonin jihohi, ‘yan majalisar dokoki, ‘yan kasuwa, abokai da masu fatan alheri da su mara wa wannan shiri baya, yana mai cewa za a bayyana cikakkun bayanai nan gaba kaɗan.
Ya jaddada cewa wannan shiri ya samo asali ne daga wajibcin ƙasa na kula da waɗanda ke sadaukar da rayuwarsu domin tsaron Najeriya, yana mai cewa tallafa musu ba sadaka ba ce, illa wajibi ne da ya rataya a wuyan kowa.
Shugaban ya ƙara da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da ƙarfafa walwala da jin daɗin dakarun soji, tare da tabbatar da cewa ana kula da su da martaba da goyon baya mai ɗorewa.

No comments