Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Ƙungiyar BudgIT Ta Yaba Wa Kaduna Kan Gaskiya da Riƙon Amana Kasafin Kuɗi

Jihar Kaduna ta samu yabo a wani sabon rahoto da ƙungiyar da ke sauƙaƙa fahimtar kasafin kuɗin gwamnati ga jama’a wato (BudgIT) ta fitar, wa...


Jihar Kaduna ta samu yabo a wani sabon rahoto da ƙungiyar da ke sauƙaƙa fahimtar kasafin kuɗin gwamnati ga jama’a wato (BudgIT) ta fitar, wanda ya nuna yadda jihar ke samun ci gaba a fannin bayyanan  kasafin kuɗin ƙananan hukumomi.

Rahoton  ya bayyana cewa Kaduna na cikin jihohi 10 kacal a fadin Nijeriya da ke samar da bayanan kasafin kudin ƙananan hukumomi a fili, abin da ke nuna ƙoƙarin gwamnati wajen inganta gaskiya da rikon amana a matakin ƙasa.

Da yake ƙarin haske akan rahoton, Kwamishinan yada labarai na jihar Kaduna, Ahmed Maiyaki, ya bayyana wannan nasara a matsayin tabbaci na salon mulkin Gwamna Uba Sani.

Ya ce: “Wannan rahoto ya tabbatar da kudirin gwamna na tabbatar da gaskiya da rikon amana a dukkan matakan gwamnati.

A cewarsa, "Ta hanyar tabbatar da cewa ana bayyana kudaden kananan hukumomi a fili, muna kara karfafa amincewar jama’a da kuma ba su damar shiga cikin harkokin mulki.”

Maiyaki ya ƙara da cewa goyon bayan da gwamnati ke bai wa cin gashin kan kananan hukumomi yana da nufin kusantar da mulki ga jama’a tare da inganta ayyukan more rayuwa.

Rahoton na BudgIT ya kuma nuna cewa Kaduna na samar da cikakken bayani kan kasafin kuɗin kananan hukumomi na matsakaicin lokaci, wanda ke bai wa jama’a da masu ruwa da tsaki damar fahimtar yadda ake tsara da rarraba kudade a fadin kananan hukumomi.

A matakin ƙasa kuwa, rahoton ya nuna cewa duk da ci gaban da wasu jihohi ke samu, da dama har yanzu na fuskantar matsalar rashin bayyana  bayanan kasafin kuɗin ƙananan hukumomi, lamarin da ke kawo cikas ga rikon amana a matakin ƙasa.

Ƙungiyar ta  BudgIT ta jaddada cewa samar da bayanan kasafin kuɗi a fili na da matuƙar muhimmanci wajen kara fahimtar jama’a kan manufofin gwamnati, da kuma karfafa sa ido da gina amincewa tsakanin gwamnati da al’umma.

Duk da wannan ci gaba, rahoton ya buƙaci a ƙara inganta yadda ake wallafa bayanan kasafin kuɗi ta fuskar daidaito, zurfi da kuma kan lokaci a dukkan jihohi.
 

No comments